Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Hamma Saleh Ya Yi Fatali da Bai Wa Pantami Takarar Gwamna a PDP
Published: May 26, 2026 at 1:23 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: May 26, 2026

Wani jigo a jam’iyyar PDP a jihar Gombe, kuma ɗaya daga cikin masu neman tikitin takarar gwamna, Alhaji Abdulkadir Hamma Saleh, ya bayyana rashin amincewarsa da matakin jam’iyyar na bai wa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami tikitin takarar gwamna.

Da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Gombe, Hamma Saleh ya ce sun shafe shekaru suna yi wa jam’iyyar hidima tare da jajircewa, don haka ba za su amince da yadda aka bayyana Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna ba tare da sahihin bayani ga masu ruwa da tsaki ba.

Ya ce ba su da wata masaniya dangane da shigowar Pantami cikin jam’iyyar PDP, illa dai kawai suka ji an bayyana shi a matsayin ɗan takarar gwamna.

Hamma Saleh ya ƙara da cewa zai bi duk hanyoyin da doka ta tanada domin kare haƙƙinsa, yana mai cewa shi cikakken ɗan jam’iyyar PDP ne wanda tun da farko ya sayi fom ɗin neman takarar gwamna.

Jigon ɗan siyasar ya kuma bayyana cewa sun san Malam Pantami ne a matsayin mamban jam’iyyar APC, kuma wanda ya taɓa neman tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar amma bai samu nasara ba.

“Idan Yace ba’ayi mishi adalci a APC ba, to Shi yayi mana adalci” Inji Hamma Saleh.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Ferfesa Pantami Yasamu Tikitin Takarar Gwamnan Gombe A Jami’yar PDP
Next Post: Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Bukaci Musulmi Su Rungumi Tausayi Da Ƙaunar Juna

Karin Labarai Masu Alaka

Yarjejeniyar Britaniya Da Mauritius Kan Tsibiran Chagos Cin Zarafi Ne Labarai
Isra’ila Zata Rusa Gidajen Da Suke Iyakarta Da Lebanon Labarai
Iran Tabada Tabbacin Cigaba Da Rufe Mashigar Hormuz Afrika
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Zuwa Jami’ar Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
CBN: An Samu Ƙaruwar Masu Cin Bashin Banki Basa Biya Najeriya
CAF Ta Dakatar Da Kocin Senegal Pape Thiaw Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Maharan Bindiga Sun Kashe Mutane 12 Masu Hakar Ma’adanai A Jihar Filato Labarai
  • Trump: Isra’ila Ta Daina Kai Hari Ga Duk Cibiyar Iskar Gas Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Hadakar Gwamnatin Najeriya Da Amurka Ne Suka Kai Hari Sokoto Najeriya
  • Gwamnatin Najeriya Tace Ta Farmaki Mayakan ISIS A Jihar Sokoto Labarai
  • Afirka Ta Kudu Ta Bayyana Yadda Aka Yaudari ‘Yan Kasar Ake Tilasta Musu Ayyukan Bauta Afrika
  • Kasar Habasha Ta Cimma Matsaya Da Masu Binta Bashi Afrika
  • Hukumar Upper Benue Zata Inganta Noma A Dadinkowa Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.