Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Matatar Man Dangote Ta Samu Tagomashi Daga Abokan Hulda
Published: December 20, 2025 at 9:31 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Matatar Man Dangote ta ƙarfafa matsayinta a matsayin babbar cibiyar rarraba man fetur a Nijeriya, bayan rage farashin man zuwa naira ₦699 kan kowace lita da kuma sauƙaƙa mafi ƙarancin adadin saye daga lita miliyan 2 zuwa lita 250,000.

Matakan sun ja hankalin ’yan kasuwar man fetur a faɗin ƙasar, inda ake samun fiye da motoci 1,000 na ɗaukar man a kullum daga matatar.

Kamfanin ya kuma ƙaddamar da tsarin garantin banki na kwanaki 10 domin tabbatar da wadatar kaya ba tare da tsaiko ba.

Shugaban Rukunin Dangote, Aliko Dangote, ya ce manufar kamfanin ita ce samar da makamashi mai rahusa kuma mai sauƙin samu ga kowane ɗan Nijeriya, yana mai jaddada cewa aikin matatar ya fi karkata ne kan bunƙasa ƙasar fiye da neman riba.

A nasu ɓangaren, Kungiyar ’Yan Kasuwar Man Fetur Masu Zaman Kansu ta Nijeriya (IPMAN) ta yi kira ga mambobinta su rika sayen man daga Matatar Dangote, tana mai tabbatar da cewa ba za a samu ƙarancin man fetur ba, duba da yadda kungiyar ke rike da sama da kashi 80 cikin 100 na kasuwar sayar da mai a fadin ƙasar.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya Ta Bawa Gwamnan Kebbi Mukamin Kyautata Harkar Kiwo
Next Post: Gwamnatin Gombe: Babu Hannun mu a Cin Zarafin Kansilan Mazabar Shamaki

Karin Labarai Masu Alaka

Gobara Ta Tashi A Makarantar Koyon Jinyar Dabbobi Dake Jihar Kano Najeriya
Gombe Ta Ƙarfafa Matasa da Ƙwarewar da Za Ta Kai Su Masana’antar Mai Da Iskar Gas Afrika
Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso Ya Fice Daga NNPP Afrika
FRSC Gombe: Hatsarin Mota Ya Yayi Ajalin Mutane 38 Ya Jikkata Fiye Da 218 A Wata Ɗaya Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Tinubu Zai Ziyarci Jihohin Borno,Bauchi Da Legas Labarai
Ana Kokarin Kawo Karshen Matsalar Kashe Matafiya A Filato Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Majalisun Najeriya Sun Amince Ta Karin Kasafin Kudi Afrika
  • An Gudanar Da Zanga-Zanga A Guinea-Bissau Afrika
  • Jam’iyyar PDP Na Kara Tsunduma Cikin Mawuyacin Hali Shirye-Shirye
  • Oliseh, Ya Ba Eric Chelle, Shawara Da Ya Zamo Mai Tsauri AFCON 2025. Wasanni
  • NAHCON Ta Kaddamar da Tawagar Malamai Afrika
  • Gwamnatin Kano Ta Rufe Gidajen Bukukuwa Da Shakatawa Labarai
  • Kasar Iceland Ta Kauracewa Bikin Gasar Wakokin Shekara Mai Zuwa Labarai
  • ‘Yan Ta’adda Sun Tarwatsa Wani Kauye A Jihar Sakkwato Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.