Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Gwamnatin Najeriya Ta Samar Da Wuta Mai Aiki Da Hasken Rana A Jami’ar ADUSTECH
Published: April 25, 2026 at 4:00 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta hannun Hukumar Makamashi ta Kasa (ECN), ta kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana (Solar) mai karfin megawatt biyu (2MW) a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote (ADUSTECH) da ke Wudil a Jihar Kano.

Wannan aiki, wanda kudinsa ya kai naira biliyan 3.8, yana karkashin shirin nan na ‘Renewed Hope Solarization’ na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Baya ga aikin samar da wutar, an kuma kaddamar da fitilun kan hanya guda 200 masu amfani da hasken rana a cikin harabar jami’ar.

Darakta Janar na hukumar, Dr. Mustapha Abdullahi, tare da Ministan Kirkira, Kimiyya da Fasaha, Kingsley Tochukwu-Udeh, ne suka kaddamar da fara aikin a ranar Juma’a.

Dr. Abdullahi ya bayyana cewa an ba kamfanin da zai gudanar da aikin wa’adin watanni uku kacal domin kammalawa. Ya ce an tsara wannan aiki ne domin kawo karshen matsalar tsadar wutar lantarki da jami’ar ke fuskanta, inda take biyan naira miliyan 22.4 a kowane wata.

“Wannan aiki na Wudil yana bin sahu ne bayan makamancinsa da muka kaddamar a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano a watan Satumban 2025, inda ake sanya tsarin megawatt hudu (4MW), da kuma aikin da muka kaddamar a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) a makon jiya,” in ji Dr. Abdullahi.

Ya kara da cewa an ba kamfanin Safiatu Global Resources Limited kwangilar a kan kudi naira biliyan 3.8, kuma ba za a kara ko sisi a kan kudin ba, sannan dole ne su kammala a cikin lokaci.

Binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa jami’ar tana da dalibai da ma’aikata sama da 24,000, kuma bukatar wutar da take da ita ta kai tsakanin megawatt 12.3 zuwa 16.4. Sai dai, wutar da take samu daga kamfanonin rarraba wuta ba ta taka kara ta karya ba, yayin da janaretocin da take amfani da su ba sa iya daukar nauyin bukatar jami’ar.

A nasa jawabin, Ministan Kirkira, Kimiyya da Fasaha, Kingsley Tochukwu-Udeh, ya ce wannan aiki mataki ne na raya kasa a karkashin manufofin gwamnatin Tinubu na bunkasa ilimi da kirkire-kirkire ta hanyar samar da ingantaccen makamashi.

Shi ma a nasa bangaren, Shugaban Jami’ar, Farfesa Musa Tukur-Yakasai, ya nuna jin dadinsa da wannan gagarumin tallafi, inda ya ce wannan mataki zai kara bunkasa harkar bincike da koyarwa a jami’ar.

Afrika, Kimiya, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Hukumar EFCC Ta Kama Dan Kasuwa A Kamaru
Next Post: Barayin Waya Sun Yanke Yatsun Hannu Guda Biyu Da Gefen Kunne A Bauchi

Karin Labarai Masu Alaka

Ranar Lahadi Anyi Zaben Shugaban Kasa A Congo Afrika
Amurka Da Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Sun Fara Wata Tattaunawa Afrika
‘Yan Bindiga A Mali Sun Kashe Direbobin Manyan Motoci Afrika
Amurka Na Shirin Kauracewa Taron Kungiyar Kasashen G20 Afrika
Amurka Zata Bawa Sojojin Najeriya Horo Labarai
CP Chuso Ya Yaba da Matakan Gwamnatin Gombe Wajen Rage Rikicin Makiyaya Da Manoma Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rwanda Tana Keta Yarjejeniyar Zaman Lafiya – Tshisekedi Labarai
  • Amurka Ta Kai Hari Kan ‘Yan ISISI A Jihar Sakkwato Bisa Rokon Gwamnatin Najeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugabar Hamayya A Venezuela Ta Gana Da Paparoma Leo Amurka
  • Za’a Jima Ana Fama Da Tsadar Farashin Mai Afrika
  • Ana Cigaba Da Ceto Masunta Daga Ruwa A Ghana Labarai
  • ‘Yan Ta’adda Sun Hallaka Sojoji Da Fararen Hula A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • Gombe Ta Yi Gasar Makarantun Firamare Don Bikin Cika Shekaru 100 Na Hassan Central Afrika
  • Shugaban Kasar Ivory Coast Yayi Sauye-Sauye A Majalisar Ministocin Kasar Siyasa
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.