Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Hukumar Raya Birane Ta Rushe Gine-Ginen Da Suka Keta Dokokin Tsara Birane A Gombe
Published: June 14, 2026 at 10:05 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Tsare-tsare da Raya Birane ta Jihar Gombe (GOSUPDA) ta ƙara ƙaimi wajen aiwatar da dokokin tsara birane, inda ta rushe wasu gine-gine da shagunan kasuwanci da aka gina ba bisa ka’ida ba a kan titin tsohon Mile uku da sauran sassan birnin Gombe.

Matakin ya biyo bayan jerin sanarwar rusau da gargaɗi da hukumar ta bai wa masu mallakar gine-ginen da abin ya shafa, tana mai umartar su da su bi dokokin tsara birane tare da cire gine-ginen da aka yi ba tare da izini ba.

Da yake magana yayin aikin rusau ɗin, Shugaban Hukumar, Alhaji Bappayo Samanja Maudo ya bayyana cewa matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da gwamnati ke yi na dawo da tsari a babban birnin jihar, tabbatar da bin ƙa’idojin gine-gine da aka amince da su, da kuma bunƙasa ci gaban birane mai ɗorewa.

Daga cikin gine-ginen da aka rushe akwai wasu shagunan kasuwanci da ke gaban Gidan rediyon Gombe waɗanda rahotanni suka nuna cewa an gina su ba tare da sahalewar hukuma ba tsawon sama da shekaru goma.

Hukumar ta ce gine-ginen sun mamaye wuraren jama’a da aka tanada tare da karya ƙa’idojin raya birane da ake aiki da su.

Haka kuma, aikin ya shafi wani wurin sayar da kaji da wasu wuraren kasuwanci da aka gina ba bisa ƙa’ida ba a kusa da otel din Jiyamare da ke yankin Tsohon Mile uku a cikin birnin Gombe.

A cewar shugaban hukumar, an gina waɗannan wurare ba tare da samun takardun izinin gini da suka dace ba, lamarin da ke kawo cikas ga tsarin raya birnin da aka tsara.

Hukumar ta sake jaddada aniyarta ta kawar da duk wasu gine-ginen da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a faɗin jihar, tare da gargaɗin mazauna jihar, masu zuba jari da masu gudanar da harkokin kasuwanci da su guji fara kowane aikin gini ba tare da samun amincewar hukumomin da abin ya shafa ba.

Ta kuma buƙaci al’umma su ba da haɗin kai ta hanyar bin dokokin tsara birane, tana mai jaddada cewa gine-ginen da ke da sahalewar hukuma kaɗai za a bari su ci gaba da kasancewa.

Hukumar ta ce manufar wannan aikin ita ce samar da muhalli mai tsari, tsaro da kyan gani ga al’ummar jihar Gombe.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Tinubu Ya Nuna Alhinin Rasuwar Janar Rabe Abubakar, Ya Jajanta wa Iyalansa
Next Post: Anyi Bikin Cikar Tsohon Shugaban Kasa Abdulsalami Shekaru 84

Karin Labarai Masu Alaka

Majalisar Kwararrun Iran Ta Sanar Da Sabon Shugaban Addini Afrika
‘Yan Jarida Sunyi Mummunan Hatsari A Bauchi Labarai
Kungiyar Tsaro Ta NATO Tana Fuskantar Kalubale Afrika
Shugaba Trump Ya Bukaci Kasar Iran Ta Mika Wuya Amurka
Gwamnatin Gombe Ta Kaddamar Da Sabon Ofishin GOGIS Don Inganta Tsarin Filaye Afrika
Hukumar ‘Yan Sanda Ta Dawo Da Dokar Zirga Zirgar Babura A Jihar Gombe Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ba Mamaki APC Ta Kafa Tarihi A Ranar Litinin Najeriya
  • NAHCON Ta Kaddamar da Tawagar Malamai Afrika
  • An Gano Kwale-Kwalen Fir’auna A Birnin Masar Afrika
  • Shugaban Amurka Yace Zasu Kakabawa Mashigar Hormuz Takunkumi Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Zata Rabawa Al’umma Tallafin Noma Afrika
  • ‘Yan Tawayen Kungiyar M23 Sun Tsagaita Sakamakon Rokon Da Amurka Tayi Amurka
  • Amurka Ta Gabatarwa Sassan Dake Yakar Juna A Sudan da Shirin Tsagaita Wuta Afrika
  • Shirin: Lafiya Jari Ce 11.21.25 Kiwon Lafiya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.