Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Sojin Saman Najeriya Sun Lalata Sansanonin ‘Yan Ta’adda
Published: May 2, 2026 at 1:56 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Sojojin saman Nijeriya sun lalata sansanonin ƴan ta’adda a Arewa maso Gabas

Rundunar Sojin Sama ta Ƙasa (NAF) ta ƙara kaimi wajen kai hare-hare ta sama kan ‘yan tada kayar baya a yankin Arewa maso Gabas, inda ta aiwatar da jerin hare-hare masu ƙarfi kan sansanonin ‘yan ta’adda a Sambisa da yankunan Tumbuns.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Hulda da Jama’a da Watsa Labarai na rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa an gudanar da wadannan hare-hare ne karkashin bangaren sama na Operation HADIN KAI.

Ya ce “bisa sahihan bayanan sirri, jiragen NAF sun kai hare-hare kai tsaye kan maboyar ‘yan ta’adda, inda suka lalata wuraren buya, suka kassara cibiyoyin kayayyaki, tare da halaka dimbin mayaka a hare-hare masu tsari da juna.”

Ejodame ya kara da cewa a ranar 30 ga watan Afrilu, “jiragen rundunar sun kai wani gagarumin harin sama a Alafa da ke yankin Sambisa, inda aka kai hari kan muhimman kayayyaki da cibiyoyin samar da kayan aiki na ‘yan ta’adda, aka kuma lalata su baki daya.”

Sanarwar ta kuma jiyo Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, yana cewa hare-haren za su ci gaba har sai an kawar da duk wata barazana.

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Sanda A Jihar Gombe Sun Karyata Kona Gidan Nafiu Bala
Next Post: Gwamna Bala Kauran Bauchi Ya Koma Jam’iyar APM

Karin Labarai Masu Alaka

An Kafa Majalisar Kotun Sulhu Ta Kano Labarai
Tattalin Arzikin Najeriya Ya Farfardo Bisa Samun Wasu Sauye Sauye Labarai
Akwai Yiwuwar Shugaban Ƙasar Afirka Ta Tsakiya Touadera Yasamu Nasara A Karo Na Uku Afrika
Dr. Kabiru Hassan Ya Kammala Wa’adinsa A GOGIS, Ya Yi Bitar Sauye-Sauyen Harkokin Filaye Afrika
Jami’yar ADC A Najeriya Ta Kori Nafiu Bala Afrika
Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Jita-Jitar Yunkurin Sanya Wa Tinubu Guba A Abinci Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno Amurka
  • Iran Ta Kama Wani Jirgin Ruwa Shake Da Mai Labarai
  • Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gargadi Jama’ar Arewa Maso Gabas Afrika
  • Matar El-Rufai Ta Roƙi Tinubu Ya Tabbatar An Yi Wa Mijinta Adalci Afrika
  • Shugaban Kasar Koriya Ta Arewa Ya Zamo Sakataren Jam’iya Mai Mulki Labarai
  • Shugabannin Darikar Anglican Sun Bada Sanarwar Kafa Sabuwar Majalisa Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Bukaci Samar Da Zaman Lafiya A Filato Afrika
  • Amurka Ta Yi Juyin Mulki A Kasar Venezuela Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.