Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Shugaba Tinubu Ya Yabawa Dakarun Tsaro Bisa Ceto Matar Marigayi Janar Rabe
Published: June 16, 2026 at 2:07 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa rundunar sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa nasarar da suka samu a wani samame da aka gudanar a Jihar Kogi, wanda ya kai ga kashe fitaccen shugaban ’yan bindiga, Ibrahim Bastuji.

A cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Litinin, Tinubu ya bayyana wannan nasara a matsayin wani babban koma baya ga ƙungiyoyin masu aikata laifuka da suka daɗe suna addabar al’ummomi a Kogi da jihohin da ke maƙwabtaka da ita.

Shugaban ƙasar ya ce Bastuji ya yi kaurin suna wajen jagorantar hare-hare, sace-sacen mutane da sauran ayyukan ta’addanci da suka jefa mazauna yankunan cikin wahala da fargaba.

Ya ce kashe shi zai taimaka wajen dawo da kwanciyar hankali tare da ƙarfafa gwiwar al’umma kan cewa hukumomin tsaro na ci gaba da samun nasara a yaƙin da suke yi da masu aikata laifuka.

“Ina taya jaruman dakarunmu murnar wannan gagarumar nasara. Najeriya ba za ta miƙa ko da inci ɗaya na ƙasarta ga masu laifi ba. Duk wanda ya zaɓi hanyar tada hankali da zubar da jinin bayin Allah, ba zai samu mafaka ba. Wannan nasara ta nuna ƙudurin jami’an tsaronmu na tabbatar da tsaro a ko’ina cikin ƙasar nan,” in ji Tinubu.

Hakazalika, shugaban ƙasar ya yabawa jami’an tsaron kan nasarar da suka samu wajen ceto Hajiya Amina Rabe Abubakar, matar marigayi tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro, Janar Rabe Abubakar mai ritaya.

Tinubu ya ce ceto ta cikin koshin lafiya ya nuna ƙwarewa, jajircewa da haɗin gwiwar da jami’an tsaro ke nunawa wajen yaƙi da masu aikata miyagun laifuka.

“Dawowar Hajiya Amina gida cikin aminci abin farin ciki ne ga iyalanta da kuma daukacin ’yan Najeriya. Ina yaba wa jami’an da suka shirya tare da aiwatar da wannan aiki cikin nasara. Hakika muna bin dakarunmu bashin godiya saboda sadaukarwar da suke yi kullum domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma,” in ji shugaban ƙasar.

Tinubu ya kuma tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da samar wa rundunar soji da sauran hukumomin tsaro kayan aiki, horo da tallafin da suke bukata domin kawo ƙarshen matsalolin ’yan bindiga, satar mutane da sauran nau’o’in aikata laifuka a ƙasar.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen yaƙi da rashin tsaro.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Sabuwar Shekarar Musulunci 1448: Kiristoci Sun Yi Murna, Sunyi Kiran Samar Da Hutu Ga Shekarar Musulunci
Next Post: Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Yan Kungiyar Lakurawa

Karin Labarai Masu Alaka

Mayakan ISWAP Sun Kai Farmaki Kan Sojojin Najeriya Najeriya
Amurka Tayi Barazanar Rage Tallafinta Wa Sudan Ta Kudu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kasar Ghana Ta Tono Gold Na Miliyoyin Kudade Kimiya
Jami’an tsaro sama da dubu biyar ne zasuyi aikin tabbatar da tsaro Alokacin bikin karamar sallah a Jihar Nejan Najeriya. Najeriya
Gwamnatin Tinubu Ta Karyata Kafa Kamfanin Gwal A Legas Labarai
Rundunar Sojin Iran Tace Harin Amurka Ya Kashe Musu Sama Da Mutane Dari Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Faransa Ta Karyata Cire Afirka Ta Kudu Daga G7 Afrika
  • Ana Cigaba Da Bincike Game Da Mutuwar Matar Da Likita Ya Manta Almakashi A Cikinta A Kano Najeriya
  • Kasar India Ta Sayi Iskar Gas Daga Iran Labarai
  • Tinubu: Mun Ware Biliyan 42 Don Inganta Lafiyar ‘Yan-Kasa Labarai
  • Gwamnatin Gombe Ta Aza Tubalin Gina Sakatariyar Gundumomin Cigaba (LCDAs) Labarai
  • Anyi Bikin Cikar Tsohon Shugaban Kasa Abdulsalami Shekaru 84 Afrika
  • CAN: Da Alamu Daliban St. Mery Na Cikin Koshin Lafiya Najeriya
  • Sunayen Jakadu: Kungiyar CISLAC Ta Nemi A Janye Sunan Mr. Ayodele Oke Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.