Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Kungiyar MDD Ta Bukaci Ayi Bincike Game Da Kashe ‘Yan Iran
Published: January 26, 2026 at 7:39 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar kula da hakkin Bil’adama ta MDD tayi Allah wadai da kasar Iran ko Farisa a ranar jumma’a, kan keta hakkin Bil’adama, kuma ta bukaci da a gudanar da bincike kan murkushe masu zanga-zanga, mataki da ya halaka dubban mutane.

Shugaban hukumar, Volker Turk, wanda ya gayawa wakilan hukumar abubuwa da suka faru a Iran, a taron ta da aka yi a birnin Geneva, ya bayyana damuwarsa kan makomar wadanda hukumomin Iran suka kama lokacin zanga zangar.

Hukumar ta amince da wani kuduri da zai fadada kudurin da ta amince dashi tun a shekara 2022 na gudanar da bincike ciki har da na yanzu, da zummmar daukar mataki nan gaba.

Iran tayi Allah wadai da wannan mataki, tana mai cewa an tsoma siyasa cikin lamarin, tana ta nanata matakan gudanar da bicike, tace wannan mataki shishshige ne cikin harkokin cikin gida. Ta kuma aza laifin tarzomar “kan ‘yan ta’adda, da masu neman tada zaune tsaye, wadanda take zargi, kan ‘yan adawar gwamnattin kasar daga ketare da kuma kasashen Amurka da Isra’ila.

Kasashe 25 ne suka amince da wannan kuduri cikin su har da Faransa, da Mexico, da koriya ta kudu, yayinda kasashe bakwai ciki harda China, da India suka ki goyon bayan kudurin, wasu kasashe 14 kuma suka kauracewa jefa kuri’a.

Kasashen China, da Pakistan, da Ethiopia, duk sun bayyana rashin gamsuwa da tasirin zaman hukumar, har jakadan China a hukumar ya kira batun, “alamarin cikin gida ne na Iran.

Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Jirgin Ruwan ‘Yan Gudun Hijira Ya Nitse Kogi A Tunisiya
Next Post: Harin Isra’ila A Gaza Da Jirgi Maras Matuki Ya Kashe Mutane

Karin Labarai Masu Alaka

Isra’ila Zata Mamaye Lebanon Labarai
Kasar Chadi Ta Rufe Iyakar Ta Da Kasar Sudan Afrika
Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed Afrika
Shugaba Tinubu Ya Kafa Kwamitin Gaggawa Akan Cutar Ebola Afrika
Hawan Babbar Sallah A Masarautar Kaltungo Dake Jihar Gombe Afrika
An Kai Hari Babbar Tashar Iskar Gas A Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ukraine Zata Sayi Iskar Gas Daga Mozambique Afrika
  • Wasan Dambe Ya Dau Sabon Salo A Jihar Inugu Wasanni
  • Jami’ai Daga Amurka Sunce Yakin Amurka Da Iran Zaizo Karshe Amurka
  • Gobara Ta Tashi A Hukumar FIRS Dake Abuja Najeriya
  • Ghana Ta Haramta Hakar Ma’adinai A Gandunan Dajin Data Kebe, Labarai
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari Afrika
  • Real Madrid: Ta Kori Xabi Alonso Bayan Rashin Nasara A Wasan Kofin Sfaniya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kungiyar ‘Yan Ta’adda Masu Alaka Da ISIS Sun Kashe Mutane A Congo Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.