Masana harkokin lafiya a jihar Gombe sun kara jaddada bukatar wayar da kai, gano cutar jijjiga ko taune-taune da wuri da kuma inganta ayyukan kula da lafiyar mata masu juna biyu domin rage mace-macen iyaye mata da jarirai da ke da alaka da cutar.
Gangamin wayar da kan wanda kwararru daga Asibitin koyarwa na tarayya Dake Gombe suka jagoranta ya kunshi kai daukin lafiya, laccoci, wayar da kai, ziyarce-ziyarce da horas da ma’aikatan lafiya a cibiyoyin lafiya goma sha daya da ke cikin birnin Gombe.

Da yake jawabi yayin bikin Ranar Yaki da Cutar Preeclampsia ta Duniya ta shekarar 2026 mai taken “San Alamomin Cutar Kuma Ka Dauki Mataki,” Babban Daraktan Asibitin, Farfesa Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da ci gaba da bai wa shirye-shiryen yaki da cutar cikakken goyon baya.
Farfesa Yusuf Abdullahi, wanda Mataimakin Babban Daraktan Asibitin, Dr. Bukar Yakubu ya wakilta, ya yabawa tawagar wayar da kai kan cutar preeclampsia bisa shirya shirye-shiryen fadakarwa da nufin ilmantar da al’umma da kuma karfafa ayyukan kula da lafiyar mata masu juna biyu.
Ya bukaci tawagar da su kara kaimi wajen fadakar da jama’a domin su fahimci illolin da cutar preeclampsia ke haifarwa, kasancewar tana daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa mace-macen mata masu juna biyu idan ba a gano ta da wuri ba.
Shugabar Tawagar Wayar da Kai Kan Cutar Preeclampsia a jihar Gombe kuma Kwararriyar Likitar Mata a asibitin, Dr. Amina Rabi’u Baba, ta ce manufar shirin shine ceto rayukan iyaye mata da jarirai ta hanyar wayar da kai da kuma kai daukin lafiya ga al’umma.
A cewarta, an fara gangamin ne da shirye-shiryen fadakarwa da kai ziyara asibitoci da cibiyoyin lafiya kafin a karkare da babban taron lacca da aka gudanar a dakin taro na Professor Idris Hall da ke Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta Gombe.
Dr. Amina ta bayyana karancin ma’aikata, rashin isasshen ilimi game da cutar da kuma jinkirin zuwa awon ciki a matsayin wasu daga cikin manyan kalubalen da ke kawo cikas wajen yaki da cutar a jihar.
A yayin ziyarar kai daukin lafiya zuwa Asibitin Town Maternity da aka fi sani da Gidan Magani, tawagar ta horas da ma’aikatan lafiya yadda za su kula da masu fama da cutar tare da bayar da kayayyakin aiki ga cibiyar.
Da yake zantawa da manema labarai yayin ziyarar, tsohon Babban Daraktan Asibitin, Professor Aliyu Usman El-Nafaty, ya bayyana cewa mata masu juna biyu karo na farko, masu fama da hawan jini, masu cutar sikila da kuma masu dauke da ciki fiye da daya na cikin wadanda suka fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar.

Ya shawarci mata masu juna biyu da su rika halartar awon ciki akai-akai domin gano matsalolin lafiya tun da wuri tare da samun kulawar likitoci yadda ya kamata.
Farfesa El-Nafaty ya kuma bukaci maza da su bai wa matansu damar zuwa asibiti domin samun kulawar lafiya a lokacin daukar ciki, yana mai cewa hakan na taimakawa wajen rage mace-macen iyaye mata da jarirai.
Shi ma da yake nasa jawabin, Dr. Ibrahim Agom da Yakubu Musa Na Magajin Garin Gombe sun gargadi maza masu hana matansu zuwa asibiti, suna mai bayyana hakan a matsayin dabi’a mai hadari ga lafiyar mata masu juna biyu.
A nata bangaren, jami’ar kula da Asibitin Town Maternity, Hajiya Zainab Umar Chiroma, ta gode wa tawagar bisa zabar cibiyar a cikin wadanda suka amfana da shirin, tare da tabbatar da amfani da kayayyakin da aka bayar yadda ya kamata.
Yayin taron fadakarwa ga mata masu zuwa awon ciki, jami’ar jinya RN Samira Salihu ta yi bayani kan hanyoyin kariya da alamomin cutar preeclampsia, tana mai bayyana cutar a matsayin babbar barazana ga lafiyar uwa da jariri.
A wajen taron karshe mai taken “Tare Za Mu Iya Ceton Rayukan Iyaye Mata Da Jarirai,” tsohon Kwamishinan Lafiya na jihar Gombe, Dr. Habu Dahiru, ya yabawa gwamnatin jihar bisa inganta ayyukan kiwon lafiya da gyaran asibitoci da cibiyoyin lafiya guda 114 a fadin jihar.

Ya bayyana cewa cutar preeclampsia cuta ce da ake iya magancewa idan an gano ta da wuri, tare da jaddada bukatar hadin kai tsakanin gwamnati, ma’aikatan lafiya da al’umma wajen rage mace-macen da ke da alaka da cutar.
A nasa jawabin mai taken “Illar Cutar Preeclampsia a Cikin Al’ummarmu,” Shugaban Kwalejin Likitanci ta Gombe State University, Professor Joshua Abubakar Difa, ya bayyana cewa cutar na haddasa matsanancin hawan jini yayin daukar ciki, lamarin da kan jefa rayuwar uwa da jariri cikin hadari.

Ya ce talauci, kiba, cututtukan koda da kuma daukar ciki fiye da daya na daga cikin abubuwan da ke kara hadarin kamuwa da cutar.
An karkare shirin da wasan kwaikwayo, daukar hotunan hadin gwiwa da kuma kira ga jama’a da hukumomi su kara himma wajen wayar da kai da inganta kula da lafiyar mata masu juna biyu domin rage mace-macen da cutar preeclampsia ke haddasawa a jihar Gombe.


