Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Baba Malam Ya Lallasa Abokan Hamayya Da Kuri’u Sama Da Dubu 236 A Zaben Fidda Gwani
Published: May 22, 2026 at 4:05 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jam’iyyar APC a jihar Yobe ta bayyana Alhaji Baba Malam a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar bayan samun rinjayen kuri’u a zaben da aka gudanar domin fitar da dan takarar jam’iyyar a zaben shekarar 2027.

Sakamakon zaben da aka sanar a zauren tattara kuri’u da ke Damaturu, babban birnin jihar, ya nuna cewa Alhaji Baba Malam ya samu kuri’u 236,711, inda ya doke sauran masu neman takarar da tazara mai yawa.

Dan takara na biyu, Dr. Abubakar Kagu, ya samu kuri’u 9,748, yayin da Bashir Machina ya zo na uku da kuri’u 1,984.

Sauran ‘yan takarar sun hada da Alhaji Hamidu wanda ya samu kuri’u 1,722, sai Modu Ma’aji da ya samu kuri’u 1,371, Mustapha Maihaja mai kuri’u 1,178, da kuma Inusa Mohammed wanda ya samu kuri’u 1,148.

Sanar da sakamakon ya gudana ne a gaban jami’an jam’iyyar, wakilan ‘yan takara da sauran magoya baya da suka hallara domin sauraron yadda zaben ya kaya.

Nasarar da Alhaji Baba Malam ya samu na nuni da irin goyon bayan da yake da shi a cikin jam’iyyar APC a jihar Yobe, yayin da ake sa ran zai jagoranci jam’iyyar a babban zaben gwamna na shekarar 2027.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: APC Ta Bayyana Abba Yusuf A Matsayin Halastaccen Ɗan Takara Bayan Cika Sharudda
Next Post: Masana Lafiya – Preeclampsia Cuta Ce Mai Hadari Amma Ana Iya Magance Ta

Karin Labarai Masu Alaka

Kama Muhyi Magaji Siyasa ce Kawai Inji Gwamnatin Kano Labarai
Jamhuriyar Nijar Ta Dakatar Da Bawa Amurkawa Visa Afrika
Hari Da Jirgi Marar Matuki Ya Kashe Mutane Da Dama A Darfur Labarai
Sakamakon Rikicin Gabas Ta Tsakiya Farashin Mai Ya Karu Labarai
‘Yan Sandan Gombe Sun Fara Kama Motocin Da Ba Su Da Lambar Rajista ko Masu Boye Lambobinsu Afrika
CHAN Ta Duba Lafiyar Idanun ‘Yan Jarida A Filato Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Bayan Shafe Shekaru Hudu A Mulki Sarkin Hausawan Ibadan Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Hare Hare A Kasar Congo Ya Jikkata Mutane Da Dama Afrika
  • Farashin Danyen Mai Ya Farfado Fiye Da Kashi Daya Sauran Duniya
  • Nnamdi Kanu Ya Nemi A Mayar Da Shi Abuja Daga Gidan Yarin Sokoto Labarai
  • Wikki Tourist FC: Ta Sallami ‘Yan Wasa Hudu Wasanni
  • Indonesia Zata Kafafa Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Gaza Labarai
  • Hukumar MDD Tace Wadanda Suka Mutu A Harin Sudan Sun Haura 70 Afrika
  • An Gano Kwale-Kwalen Fir’auna A Birnin Masar Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.