Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Kasar Uganda Ta Tsare ‘Yan Jam’iyyun Adawa Dubu Biyu
Published: January 23, 2026 at 8:04 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Chief Muhoozi Kainerugaba, shugaban dakarun sojojin Uganda, kuma da ga shugaba Yoweri Museveni, ya ce hukumomin kasar suna tsare da magoya bayan jam’iyyun adawa 2000, tare da hallaka 30, kuma suna farautar wasu, biyo bayan zaben shugaban kasa da ake kalubalantar nasarar Yoweri Musaveni.

Yoweri Museveni, ya rike ragamar mulkin kasar har kusan tsawon shekaru 40. A zaben da aka gudanar ranar 15 ga Watan Janairun nan ma, hukumar zabe ta ce shi yaci zaben, inda ya bawa babban dan adawa Bobi Wine na jam’iyyar National Unity Platform, wato NUP tazara sosai wajen yawan kuri’u.

Bobi Wine, wanda da mawaki ne, ya zamo dan siyasa, kuma sunan sa na asali Robert Kyagulanyi, ya ki amincewa da sakamakon zaben, inda yayi zargin an tafka magudi, kuma daga nan ya shiga buya.

A wasu sakonni da ya wallafa a shafin sada zumunta cikin dare shugaban dakarun sojojin na Uganda, kuma da ga Museveni, ya bayyana yadda aka gudanar da kame tare da kashe wasu magoya bayan jam’iyyar NUP, inda ya alakanta su da bata gari, kuma ‘yan ta’adda.

Gwamnati ta zargi Magoya bayan Wine da tada hargitsin zabe, shi kuma a nasa bangaren ya ce jami’an tsaro ne suka far ma magoya bayan nasu. Kamfanin dillacin labarai na Reuters bai samu damar samun sahihancin wadannan zarge-zarge ba.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Gwamnan Jihar Kano Ya Fice Daga Jam’iyar NNPP
Next Post: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane A Wajen Hakar Ma’adanai Dake Jihar Filato

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Tayi Barazanar Rage Tallafinta Wa Sudan Ta Kudu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gidauniyar Jalo Wali Ta Ƙaddamar Da Bada Audugar Mata A Gombe Afrika
Samar Da Tsaro A Jihar Kano Ba Sai An Sa Siyasa Ba! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Rundunar ‘Yan Sandan Kebbi Ta Dakile Yunkurin Garkuwa Da Mutune, Ta Kama Masu Laifi Afrika
Gwamnatin Kasar Benin Ta Nemi ‘Yan Kasa Su Kwantar Da Hankali Afrika
Sabuwar Sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Za Ta Ƙarfafa Ayyukan Ci Gaban Yankin Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sallah Sai Ranar Juma’a A Najeriya: Fadar Sarkin Musulmi Afrika
  • Ministan Kudin Najeriya: Bamu Samu Kudaden Da Muke Tsammani A Wannan Shekarar Ba Najeriya
  • Shugaban Miyetti Allah Zai Fuskanci Shari’a Kan Zargin Badakalar Kuɗi da Ta’addanci Afrika
  • Sojoji Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda a Kukareta Afrika
  • Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Yayi Ajalin ‘Yan Ghana 50 Afrika
  • Baitul Malin Amurka Zata Bawa Venezuela Da Cuba Damar Sayar Da Mai Amurka
  • Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Ya Zamo Khalifan Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Jefa Makamin Tomahawk A Makarantar Yara Mata Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.