Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi Afrika
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya Afrika
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91 Afrika
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu Afrika
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika

AFCON 2025, Jerin Abubuwan Da Aka Haramta Wa Magoya Baya
Published: December 15, 2025 at 7:18 PM | By: Bala Hassan

­Jerin abubuwan da a ka haramta wa magoya baya su shiga da su filayen wasa lokacin gasar cin kofin kasashen afirka da za’ayi na 2025, a Morocco.

A yayin da ake shirye-shiryen Gasar kwallon kafa mafi girma ta Afirka, AFCON 2025, wadda za ta fara a ranar Lahadi, 21 ga Disamba 2025 wacce Morocco, zata karbi bakunci.

Inda masu masaukin baki Kasar Morocco za su fafata da Comoros a wasan farko a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke Rabat,  za a fara wasan da karfe 8 na dare agogon Najeriya, Nijar Kamaru da Chadi, dai dai da 19:00 na dare agogon GMT.

An gargadi magoya bayan da zasu halarci wasanni game da jerin abubuwan da aka haramta musu shiga da shi filin wasa yayin gasar.

Ba a yarda da wasan wuta, fasahar na’urorin laser, abubuwa masu kaifi, gilashi, da makame ba, har ila yau an haramta shiga da sigari, barasa, da miyagun kwayoyi.

An kuma haramta amfani da kayayyakin da ke dauke da sakonnin batanci da basu dace ba.haka zalika ba za’a bar manyan abubuwa da suka kai santimita 40 a cikin filayen wasa ba.

Wannan ya haɗa da keken motsa jiki, manyan laima, dabbobi, da tutoci masu girma.

An haramta busa, ƙaho, fitilu, ashana, tabarau masu kyamarori na ƙwararru, da kayan rikodi. An haramta amfani da abin rufe fuska, feshi iskar gas, da duk wasu abubuwan da ake ganin yana nuna wariya, cin zarafi, ko kuma siyasa.

Birni shida za su karɓi baƙuncin wasanni a lokacin gasar. An zaɓi Rabat, Casablanca, Marrakech, Agadir, Fès, da Tangier bisa ga ƙa’idodin filin wasa.

Jimillar ƙungiyoyi 24 zasu fafatawa, waɗanda aka raba zuwa rukuni shida mai dauke da ƙungiyoyi huɗu.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: Rikici Ya Barke A Kano Bayan Kashe Wani Matashi Da Ake Zargi Da Kashe Ladani
Next Post: Tinubu: Zamu Kara Kyautata Samar Da Kayan Aiki Ga Jami’an Tsaro

Karin Labarai Masu Alaka

Kocin Newcastle Matthias Ya Ce Lewis Hall Ba Zai Koma Manchester United Ba Wasanni
Ahmed Musa, Yayi Ritaya A ƙwallon ƙasa Da ƙasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Tabbas Za’a Gudanar Da Gasar Firimiya Lig Ta Najeriya Wasanni
CAF Ta Yanke Hukunci Kan Ƙasashen Senegal Da Moroko AFCON 2025 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Wikki Tourists FC: Ta Yi Sabbin ‘Yan Wasa Uku Wasanni
An Bude Gasar Kwallon Kafa Ta Mata A Najeriya NWFL 2025 Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Iran Zata Sassauta Shirin Nukiliya Tsakaninta Da Amurka Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan-Ta’adda Sun Kara Sace Mutane A Jihar Naija! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasar Amurka Da Rasha Zasu Kawo Karshen Tsagaita Nukiliya Amurka
  • Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Tura Sojoji Benin Labarai
  • Na Duke Tsohon Ciniki Shirye-Shirye
  • Farashin Danyen Mai Da Iskar Gas Ya Tashi Afrika
  • Gwamnatin Tarayya Tayi Baje Kolin Nasarorin Tinubu Afrika
  • ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayin Shanu Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.