Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
  • Hukumomin Kashe Gobara A Gombe Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Hana Gobara A Lokacin Bazara Labarai

Fanny Amun Ya Yi Murabus A Matsayin Shugaban Kwamitin Binciken NFF
Published: August 25, 2026 at 8:34 PM | By: Bala Hassan

Fanny Amun Ya Yi Murabus A Matsayin Shugaban Kwamitin Binciken NFF

Ambassador Fanny Amun ya yi murabus daga matsayin shugaban kwamitin binciken Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF), bayan kammala aikinsa da mika rahoton kwamitin.

A cewar rahoton Brila Media, Amun ya sanar da cewa ya bar mukamin ne bayan kwamitin ya kammala aikin da aka dora masa, yana mai cewa ba ya son ci gaba da zama a matsayin bayan mika rahoton domin kauce wa duk wani yanayi da zai iya haifar da zargin yin katsalandan ko rashin gaskiya.

NFF ta kafa kwamitin mai mambobi shida a ranar 17 ga watan Agusta domin gudanar da bincike kan matsalolin da suka janyo koma bayan kungiyoyin kwallon kafar Najeriya a wasannin kasa da kasa, tare da gabatar da shawarwari kan yadda za a inganta tafiyar da kungiyoyin kasar.

Daya daga cikin muhimman abubuwan da kwamitin ya mayar da hankali a kansu shi ne rashin nasarar Super Falcons wajen samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA ta 2027.

Super Falcons ta kasa samun gurbin kai tsaye zuwa gasar bayan da Kamaru ta fitar da Najeriya a wasan daf da na kusa da na karshe na gasar WAFCON, kafin daga bisani Afirka ta Kudu ta doke Najeriya da ci 2-1 a wasan neman gurbin shiga matakin **Inter-Confederations Playoffs**.

Sakamakon haka, Najeriya za ta iya rasa gasar cin kofin duniya ta mata a karon farko tun bayan fara gasar a shekarar 1991.

Amun ya samu hadin gwiwar tsohon kocin kungiyar Flying Eagles, Ladan Bosso; tsohuwar kyaftin din Super Falcons, Desire Oparanozie; tsohon kyaftin din Super Eagles, Mutiu Adepoju; tsohon alkalin wasa na FIFA, Dr Alex Mana; yayin da Nasiru Sa’idu ya kasance sakataren kwamitin.

Rahoton kwamitin yanzu yana hannun NFF domin duba shawarwarin da aka gabatar da kuma daukar matakan da suka dace kan makomar kwallon kafar Najeriya.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna
Next Post: Feyenoord Ta Fara Tattaunawa Da Manchester United Kan Daukar Chido Obi Aro 

Karin Labarai Masu Alaka

NFF Ta Nemi Afuwar Tinubu Da ’Yan Najeriya Kan Rashin Samun Tikitin Zuwa Gasar Kofin Duniya Ta Mata Wasanni
Uefa Ta Zabi Artan, Ya Jagoranci Wasan Cin Kofin Uefa Super Cup Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
FIFA Ta Ba Da Goyon Bayanta Ga Gyaran Ƙwallon Ƙafa A Najeriya, Shehu Dikko Ya Gana Da Infantino Wasanni
FIFA Ta Buɗe Bincike Kan Koci Hossam Hassan Na Masar Wasanni
Da Alamu Ronaldo Zai Buga Dukkan Wasanni Da Gasar Kofin Duniya A 2026 Wasanni
Galatasaray Ta Yi Watsi Da Tayin €150m Daga Al-Hilal Kan Victor Osimhen Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
  • Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jami’ai A Mexico Sun Tabbatar Da Kashe Shugaban Masu Shan Ƙwaya Nemesio Oseguera Labarai
  • Gwamnatin Najeriya Ta Jinjinawa Saudiya Afrika
  • Ƙarin Albashi Zai Fara Aiki Ga Sojojin Najeriya Daga Satumba Afrika
  • Manchester United: Za Ta Nada Michael Carrick A Matsayin Kocin Riƙon ƙwarya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Allah Ya Yi Wa Sheikh Dahiru Bauchi Rasuwa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • EFCC Ta Tsare Tsohon Minista Abubakar Malami Tsaro
  • Kasar Amurka Takara Saka Takunkumi Akan Kasar Venezuela Amurka
  • Jirage Marasa Matuka Sun Kaiwa Jiragen Ruwan Mai Hari A Gulf Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.