Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

EFCC Ta Tsare Tsohon Minista Abubakar Malami
Published: December 10, 2025 at 1:51 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Tsohon Antoni Janar kuma ministan shari’ar Najeriya Abubakar Malami, ya shafe kwana na biyu a tsare a hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) bayan kasa cika sharuddan belinsa.

Majiyoyi sun ce ana bincikensa kan zarge-zargen laifuka 18, ciki har da hada hadar kuɗi da saba ka’idar aikin ofis, da kuma zargin taimakawa ayyukan ta’addanci ta hanyar kuɗi.

Hakanan, ana tuhumar sa kan yadda aka yi asarar dala miliyan $346.2 na kudin Abacha da aka dawo dasu daga Switzerland da Jersey, da kuma rabon kudaden shirin Anchor Borrowers na Naira biliyan 4.

EFCC na kuma binciken zargin cewa Malami ya zuba Naira biliyan 10 a makarantu, otal-otal da injinan shinkafa a Kebbi, tare da duba akalla asusun banki 46 da ake zargin suna da alaka da shi.

Malami, wanda ya koma jam’iyyar ADC a 2025, ya bayyana aniyarsa ta takarar gwamnan jihar Kebbi a 2027.

Jaridar The Cable ta kuma tunatar da wasu manyan mu’amaloli biyar da ake zargin sun faru a lokacin da Malami ke ofis, ciki har da biyan dala miliyan $496 ga GSHL a batun Ajaokuta, da sayar da kadarorin da aka kwace, da kuma rikicin biyan dala miliyan $419 ga masu neman diyya na Paris Club.

Tsaro

Post navigation

Previous Post: Ganduje Ne Yasa Aka Kama Ni Inji Muhuyi Magaji
Next Post: Soyinka Ya soki Yawan Jami’an Tsaron Da Ake Bai Wa Seyi Tinubu

Karin Labarai Masu Alaka

Wani Bayahude Ya Harbe Bafalatsine Dan Shekaru 16 Tsaro
‘Yan Ta’adda Sun Kashe ‘Yan Sanda A Jihar Katsina Najeriya
Dakarun Operation Fansan Yamma Sun Ceto Mutane 48 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Afrika
Kaduna: Masana Sun Nemi A Sauya Tsohon Wurin Zubar Da Shara Na Tudun-Ilu Afrika
Amurka Da Kasashen Yamma Suna Cigaba Da Kai Ruwa Rana Akan Nukiliyar Iran Afrika
EU Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Amurka Da Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gaza Ga Albarusai Ga Yunwa Tsaro
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Kamfanin Mai Mallakar Saudiya Aramco Zai Sanja Hanyar Fitar Da Danyen Mai Labarai
  • Jami’ar ABU Zaria Ta Karbi Kudade Naira Bilyan 1.3 Daga Shirin Nelfund Afrika
  • Majalisar Dokokin Rivers Zata Tsige Fubara Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaban Amurka Yayi Watsi Da Tattaunawar Kawo Karshen Yaki Da Iran Afrika
  • Taron Sulhu Tsakanin Addinai Mabanbanta Na Arewacin Najeriya Labarai
  • INEC: Akwai Yiwuwar Dage Zaben 2027 Saboda Azumi Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.