Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Papa Roma Leo Yace Zai Cigaba Da Sukan Yake Yake
Published: April 14, 2026 at 8:32 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Papa Roma Leo, ya fadawa kamfanin dilancin labarai na Reuters cewa zai ci gaba da suka kan dukkan wani matakin yaki, bayanda shugaba Donald Trump ya caccaki shugaban darikar katholika mai mabiya bilyan daya da milyan dari hudu a fadin duniya.

A kalamai da yayi cikin jirginsa kan hanyar sa ta zuwa birnin Algiers, inda ba Ameriken Papa Roman zai fara ziyarar aiki na kwana 10 zuwa kasashen Afirka hudu, shugaban darikar katholikan yace ana wargi da koyawar masihanci.

“Bana so mu shiga muhawara dashi, Leo ya gayawa Reuters, yayinda yake gaida ‘yan jarida da suke tare da shi, “Bana jin sakon addinin kirista abun wasa bane, kamar yadda wasu mutane suke yi.”

“Zan ci gaba da magana da babban muriya kan yaki, da nufin wanzar da zaman lafiya, da tuntubar juna, da mu’amala tsakanin kasashe, domin samun hanyoyin warware matsaloli, inji PapaRoma a magana da yayi cikin harshen turanci.

“Mutane masu yawan gaske suna wahala sosai a duniya a yau,” inji Papa Roma Leo, ana kashe mutane masu yawan gaske wadanda basu aikata laifin komi ba, saboda haka nake gani akwai bukatar wani ya tashi tsaye domin acewarsa, akwai wata hanya da ta fi dacewa.

Sakon coci, da sakona, da sakon linjila shine, “Allah ya sanya albarka ga masu wanzar da zaman lafiya. Bana kallon matsayina a zaman siyasa ko dan siyasa, inji Papa Roma Leo.

Papa Roma Leo, wanda dan asalin birnin Chicago ne a Amurka, ya kasance babban mai sukar yakin Amurka da Isra’ila kan Iran a makonnin baya bayan nan.

Abunda yasa shugaba Trump ya caccaki shi a zaman martani kan sukar da Papa Roman yake kan yakin na gabas ta tsakiya.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Kawayen Amurka Bazasu Shiga Matakin Shugaba Trump Ba
Next Post: Zabebben Shugaban Hungary Yace Zaidawo Da Tsarin Dimokraɗiyya

Karin Labarai Masu Alaka

Jama’a A Yankin Gulf Sun Bukaci Dakatar Da Hare Hare Daga Washington Afrika
Zulum Ya Rushe Majalisar Zartarwa Ta Jihar Borno Afrika
Shugaba Trump Ya Bukaci Kasar Iran Ta Mika Wuya Amurka
Tinubu Ya Kafa Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Afrika
Shugaban Kasar Uganda Yana Kokarin Mayar Da Mulkin Kasar Na Gado Labarai
Amurka Zatayi Amfani Da Sansanonin Birtaniya Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sarkin Musulmi Ya Ziyarci Shugaba Bola Tinubu Afrika
  • Sanata Sa’idu Alkali Ya Kaurace Wa Zaben Fidda Gwani Afrika
  • Guinea Bissau Ta Tsaida Gwaje-Gwajen Allurar Rigakafin Shawara A Kasar Labarai
  • Gwamnatin Najeriya Tace A Maboyar ‘Yan Ta’adda Aka Kai Harin Jilli Afrika
  • Gwamnan Jihar Kano Ya Fice Daga Jam’iyar NNPP Siyasa
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika
  • Magoya Bayan Manchester United Sun Bukaci A Siyar da Bruno Fernandes Bayan Rashin Nasara A Kan AC Milan Wasanni
  • Kasar Gambiya Ta Gayawa Kotun MDD Shirin Myanmar Akan Musulmai Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.