Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Matar El-Rufai Ta Roƙi Tinubu Ya Tabbatar An Yi Wa Mijinta Adalci
Published: July 8, 2026 at 9:29 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Matar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai, ta yi kira ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya tabbatar an yi wa mijinta, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, adalci yayin da yake fuskantar shari’ar da ake yi masa.

Da take magana a ranar Talata a gidan iyalansu da ke Abuja tare da ɗayar matar El-Rufai, Hajiya Aichatou El-Rufai, Asia ta ce ba sa roƙon Shugaban Ƙasa ya tsoma baki a cikin shari’ar, sai dai su tabbatar an mutunta haƙƙoƙin El-Rufai da kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada.

Ta tuna irin goyon bayan da ita da mijinta suka bai wa Tinubu a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, tana mai cewa sun yi aiki tuƙuru domin samun nasararsa a Jihar Kaduna.

“Mai Girma Shugaban Ƙasa, na yi muku yaƙin neman zaɓe. Na zagaya ko’ina cikin Jihar Kaduna domin neman muku ƙuri’u. Mijina ya tsaya tsayin daka tare da ku. Shin wannan ne sakamakon da iyalinmu suka cancanta?” in ji ta.

Asia ta roƙi Shugaban Ƙasa da ya tabbatar an bai wa El-Rufai damar samun kulawar lafiya, ganawa da lauyoyinsa da kuma iyalansa, tana mai jaddada cewa abin da suke nema shi ne adalci da kuma mutunta doka.

“Ba na roƙon ku ku hana a gurfanar da shi a kotu ba, abin da muke nema shi ne a ba shi haƙƙoƙin ɗan Adam na asali da Kundin Tsarin Mulkin da kuka rantse za ku kare ya tanada,” in ji ta.

Ta kuma yi zargin cewa El-Rufai, wanda ta ce likitoci sun tabbatar yana fama da hawan jini da kuma ciwon sukari, ba ya samun isasshiyar kulawar lafiya yayin da yake tsare.

A cewarta, hana likitansa na kashin kansa, lauyoyinsa da ‘yan uwansa damar ganinsa ya jefa iyalan cikin damuwa matuƙa.

“Mu iyalansa muna cikin firgici. Muna rayuwa cikin fargabar wata rana mu wayi gari da labarin da ba ma fatan ji,” in ji ta.

Asia ta ce ya kamata a bai wa mijinta damar kare kansa yadda ya kamata yayin da shari’arsa ke gudana.

“Ya kamata a ba shi beli cikin sharuddan da suka dace. Idan yana da laifi, kotu ce za ta yanke hukunci. Idan kuma ba shi da laifi, ita ma kotu ce za ta tabbatar da hakan,” ta ƙara da cewa.

Wannan roƙo ya biyo bayan kama likitan El-Rufai, Bello Abubakar, da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka masu Alaƙa (ICPC) ta yi bisa zargin bayar da bayanan da ake zargin ba daidai ba ne game da ziyarar duba lafiyar tsohon gwamnan yayin da yake tsare.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Sarakunan Gombe Da Zazzau Sun Yi Kira Ga ‘Yan Najeriya Su Rungumi Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
Next Post: Gwamnonin Arewa Sun Kaddamar da Kwamitin Asusun Tsaro

Karin Labarai Masu Alaka

SERVICOM, ATBUTH Ta Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Damfara Ne Labarai
EU Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Amurka Da Iran Afrika
Kungiyoyin Mata A Jihar Filato Sunyi Gangamin Samun Jagorancin Siyasa Afrika
Gwamnatin Tarayyar Najeriya Zata Raba Taki Ga Manoma Afrika
Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki Labarai
Dan Gudun Hijira Tarique Rahman Ya Kusa Zama Shugaban Kasa Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Zata Samar Da Sabbin Dakunan Karatun Dalibai Afrika
  • Trump: Zamu Kawo Zaman Lafiya A Fadin Duniya Amurka
  • Salmanu: Ci Gaban Wikki Tourist FC Shine A Gaba Na Wasanni
  • Kasar Saudiya Ta Sanar Da Ganin Watan Azumi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Sanda A Finland Sun Kwace Jirgin Ruwan Kasar Rasha Afrika
  • Tinubu Na Kokarin Rage Tsadar Sufuri Ta Hanyar Shirin CNG Afrika
  • Zamu Hana Wasu ‘Yan-Najeriya Visa Shiga Amurka Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.