Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

‘Yan Kasar Venuzuela Zasu Fara Komawa Gida
Published: January 21, 2026 at 9:50 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wasu ‘yan asalin kasar Venezuela da suka yi kaura suka bazu kasashen da ke yankin kudancin Amurka, sun fara tunanin ko su koma gida tun bayan hambarar da shugaba Nicolas Maduro daga mulki, inda suke fatan za’a gabatar da zaben sabuwar gwamnati bisa tsarin demokradiya wadda zata magance rugujewar tattalin arzikin kasar.

A kalla Kashi 25 cikin dari na ‘yan kasar Venezuela sun yi kaura zuwa kasashen dake yankin kudanci Amurka, Caribbean, Spain da kuma kasar Amurka tun shekarar 2014, inda suka gujewa rushewar tattalin arzikin kasar da ta dogara da man fetur, sakamon rikon sakaina daga gwamnati.

Wani likita Juan Carlos Viloria, da ke zaune a kasar Colombia, kasar da ke dauke da mafi Yawan ‘yan gudun hijira daga Venezuela, ya ce ya na so, ya koma kasar sa, domin bada gudummawar sa wajen farfado da ita.

Amma kuma ci gaba da rike ragamar mulki da matamakiyar Nicolas Maduro, Delcy Rodriguez ke yi gam, da jin tsoron samun ci gaba da danniya daga gwamnati, da gurbacewar tattalin arziki, na sa mutane tsoron komawa. Ya kara da cewa mazauna arewa maso gabashin Colombia da yake aiki da su, sun lura akwai karin mutanen dake ratsowa cikin kasar daga Venezuela suyi aiki don su samu kudi, kafin abubuwa suyi sauki a Venezuela.

Amurka

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Sham Tace Harin Kurdawa Ya Hallaka Sojojin Kasar
Next Post: Shugaban Amurka Donald Trump Ya Nanata Aniyar Mallakar Greeland Daga Kasar Denmark

Karin Labarai Masu Alaka

Kasashen Amurka Da China Sun Matsawa Ghana Domin Rage Kudaden Haraji Afrika
Afirka Ta Kudu Tace Bazata Yanke Alaka Da Iran Ba Afrika
Kasar Amurka Takara Saka Takunkumi Akan Kasar Venezuela Amurka
Jamhuriyar Nijar Ta Dakatar Da Bawa Amurkawa Visa Afrika
Shugaban Kasar Ghana Ya Soki Manufofin Gwamnatin Amurka Afrika
An Yi Fashin Kaguwa Da Dodon-Kodi Na Miliyoyin Dalar Amurka Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sarkin Musulmi Yayi Magana Game Da Matsalar Tsaron Kasar Tsaro
  • Mahaifiyar Nasiru El Rufai Ta Rasu Afrika
  • Shirin Ga Fili GA Doki Shirye-Shirye
  • Isra’ila Zata Mamaye Lebanon Labarai
  • Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Bukaci Musulmi Su Rungumi Tausayi Da Ƙaunar Juna Afrika
  • Gwamnatin Tinubu Ta Karyata Kafa Kamfanin Gwal A Legas Labarai
  • Taron Sulhu Tsakanin Addinai Mabanbanta Na Arewacin Najeriya Labarai
  • Jirgin Ruwan ‘Yan Gudun Hijira Ya Nitse Kogi A Tunisiya Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.