Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata Afrika
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa Afrika
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno Amurka
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe Afrika
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya Afrika

Ministan Tsaro Ya Umarci Janye Sojoji Daga Shingayen Bincike A Tituna
Published: December 12, 2025 at 11:20 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: December 12, 2025

Ministan tsaro ya umarci janye sojoji daga shingayen bincike a Titunan kasar.

Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya bayar da umarnin gaggawa na janye dakarun sojoji daga wuraren binciken ababan hawa da ke manyan tituna a sassa daban-daban na ƙasar.

Ya bayyana cewa wannan matakin na da nufin mayar da hankali kan yaƙi da ’yan ta’adda da sauran barazanar tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, inda jami’an ’yan sanda za su karɓi ragamar kula da shingayen tituna da tsaron ababan hawa.

Ministan ya ce sojoji za su koma ayyukan su na ƙwarai na yaƙi da ta’addanci da samar da tsaro a yankunan da ke fama da barazana, musamman Arewa maso Gabas da wasu sassan Arewa ta Tsakiya.

Ya kuma jaddada cewa hakan ba yana nufin raguwar tsaro ba ne, domin an tsara yadda za a maye gurbin sojojin da jami’an ƴan sanda da suka samu horo musamman kan kula da jama’a da tabbatar da doka a tituna.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Atiku Ya Zargi Gwamnati Da Kama ‘Yan Adawa
Next Post: Shirin Manuniya Yau Juma’a 12.12.2026

Karin Labarai Masu Alaka

Sallah Sai Ranar Juma’a A Najeriya: Fadar Sarkin Musulmi Afrika
Shari’ar Abubakar Malami Ta Kaura Zuwa Sabon Alkali Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani Afrika
An Bukaci Matasa Su Taka Gagarumar Rawa Wajen Gina Zaman Lafiya A Arewa Maso Gabas Afrika
Tinubu Ya Rantsar Da Shugabar Hukumar FCC Najeriya
An Kashe Mutane 25 Yayin Kai Wasu Hare Hare Jihar Adamawa Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tinubu: Abba Magajin Aminu Kano Ne A Fagen Siyasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Tsinto Gawarwakin ‘Yan gudun Hijira A Bakin Tekun Comoros Labarai
  • Anyi Rashin ‘Yan Jarida 6 A Jihar Gombe Sakamakon Hatsarin Mota Labarai
  • Kamfanin Hakar Ma’adanai Na Kasar Kanada Ya Cigaban Da Aikinsa Labarai
  • Gwamnatin Kano Ta Rufe Gidajen Bukukuwa Da Shakatawa Labarai
  • Bankin Duniya Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Afirka Da Yankin Sahara Afrika
  • Motsepe, Daga 2028 AFCON Zata Sauya Daga Shekaru Biyu Zuwa Hudu Wasanni
  • Amurka Ta Girke Jirage Marasa Matuki Tare Da Sojoji A Najeriya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.