Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Zargin Fitar Da Bayanan Masu Zabe A Najeriya
Published: June 3, 2026 at 1:17 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta a Najeriya (INEC), ta ce ta fara bincike kan zargin fitar da bayanan wani ɗan takara daga kundin rajistar masu kaɗa ƙuri’a (CVR), yayin da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, (DSS), ita ma ta fara nata binciken.

INEC ta bayyana cewa binciken farko ya nuna babu wani kutse daga waje ko harin na’ura mai kwakwalwa da ya shiga tsarin bayananta. Sai dai an samu damar shiga bayanan ne ta hanyar sahihan bayanan shiga da aka bai wa wasu jami’an rajistar masu zaɓe, amma aka fitar da bayanan ba tare da izini ba.

Hukumar ta ce ta gano asusun da aka yi amfani da shi wajen shiga bayanan, kuma tana binciken ko an karya dokokin tsaro da kariyar bayanai. Ta kuma tabbatar da cewa lamarin bai shafi bayanan sama da masu zaɓe miliyan 90 da ke cikin kundinta ba.

Sai dai ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce bayanin da INEC ta fitar ya ƙara haifar da tambayoyi fiye da amsoshi. Ya buƙaci a yi cikakken bincike domin gano yadda bayanan da ke cikin tsarin da aka killace suka kai hannun wasu ‘yan siyasa.

Atiku ya ce rashin samun kutse daga waje ba ya rage girman lamarin, domin hakan na nuna yiwuwar matsalar ta fito daga cikin tsarin hukumar. Ya kuma yi maraba da binciken DSS, yana mai cewa dole ne a gudanar da shi cikin adalci ba tare da nuna son kai ba.

Takaddamar ta samo asali ne bayan mai taimaka wa Ministan Abuja kan harkokin yaɗa labarai, Lere Olayinka, ya wallafa bayanan rajistar zaɓe na fitaccen jarumin Nollywood, Emeka Ike. Jarumin ya yi zargin cewa an karya masa haƙƙin sirri, tare da barazanar ɗaukar matakin shari’a kan lamarin.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: NAHCON Ta Fara Shirye-shiryen Dawowar Alhazai
Next Post: An Fara Dawo Da Alhazain Najeriya Gida

Karin Labarai Masu Alaka

Aisha Buhari Ta Bayyana Irin Kalubalen Da Ta Fiskanta Sakamakon Biyewa Jita-Jita Labarai
Afrika Ta Kudu Ta Dora Haraji Mai Yawa Kan Karafa Afrika
Yakin Gabas Ta Tsakiya Ya Haifar Da Tsadar Taki Da Mai Ga Manoma Labarai
Gwamna Inuwa Yahaya Ya Jaddada Haƙuri Da Fahimtar Juna A Siyasa Afrika
KADCCAM Ta Yaba Da Shuka Bishiyoyi A Kaduna Afrika
Shugaba Tinubu Ya Tafi Kasar Faransa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kungiyar Kwadago Ta NLC Ta Gudanar Da Zanga-Zanga Bisa Matsalar Tsaro Tsaro
  • Amurka Ta Kama Tsohon Ministan Kudin Kasar Ghana Afrika
  • Amurka Ta Cire Takunkumin Da Ta Kakabawa Shugaban Venezuela Amurka
  • Kasar Zimbabwe Ta Samar Da Dokar Tsawaita Mulkin Mnangagwa Zuwa 2030 Labarai
  • Dakarun Operation Fansan Yamma Sun Ceto Mutane 48 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Afrika
  • Najeriya Tayi Asarar Kusan Naira Triliyan 1 Sakamakon Harajin Trump Amurka
  • Fiye Da Mutane 10 Sun Mutu A Hatsarin Hanyar Kano Labarai
  • Tsohon Dan-Takarar Gwamnan PDP A Gombe Ya Shiga ADC Siyasa
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.