Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata Afrika
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa Afrika
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno Amurka
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe Afrika
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya Afrika

Iran Tace Farisa Zata Kai Hari Kan Mayakan Amurka
Published: February 8, 2026 at 10:16 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ministan harkokin wajen Iran ya fada ranar Asabar cewa, Farisa zata kai hari kan sansanonin mayakan Amurka da suke gabas ta tsakiya, ministan wanda yayi magana ranar Asabar yace kada a dauka matakin a zaman kai hari ga kasashen da suka bada masauki ga dakarun na Amurka ba.

Ministan harkokin wajen Abbas Araqchi, wanda yayi magana da tashar talabijin ta Aljazeera, kwana daya bayan da hukumomin Iran da Washington suka ce za su ci gaba da tattaunawar da suke yi ba kai tsaye ba, game da shirin Nukiyar kasar, tattaunawar da duka bangarorin biyu suka yaba dashi a zaman da suka yi a ranar jumma’a a Oman.

Araqchi yace ba’a tsaida rana domin ci gaba da tattaunawar ba, amma shugaba Trump yace za’a yi zagaye na biyu na shawarwarin a farkon mako mai zuwa, ministan harkokin wajen yace duka sassan biyu sun amince da yin haka ba tare da bata lokaci ba.

Shugaba Trump yayi barazanar zai kai wa Iran hari bayan da Amurkan ta jibge jiragen yakin ruwa a yankin, inda ta bukaci Iran ta daina sarrafa ma’adinan Uranium, da zai bata damar kera makamin Nukiya, da kuma tsaida kera makamai masu linzami, da kuma ta daina bada goyon bayan da take yi ga kungiyoyin ‘yan tawaye a yankin.

Yayinda duka sassan biyu suka nuna a shirye suke su farfado da shawarwari kan shirin nukiliyar kasar da take rigima da kasashen yamacin duniya akai, Araqchi yaki ya amince a fadada batutuwa da shawarwarin zai taba.

Amurka, Labarai

Post navigation

Previous Post: Kasar Aljeriya Ta Soke Yarjejeniyar Jirgin Sama Tsakaninta Da Daular Larabawa
Next Post: Anyi Janazar ‘Yan Shi’a 33 Da Aka Kashe A Masallacin Juma’a

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaban Ukraine Ya Tattauna Da Trump Akan Zaman Lafiya Amurka
Iran Zata Mayarwa Amurka Martanin Harin Kharg Afrika
Papa Roma Leo Yace Zai Cigaba Da Sukan Yake Yake Afrika
Dr. Kabiru Hassan Ya Kammala Wa’adinsa A GOGIS, Ya Yi Bitar Sauye-Sauyen Harkokin Filaye Afrika
Shugabannin Sojojin Najeriya sun Kai Ziyarar Aiki Maiduguri  Afrika
Hukumar ICPC Ta Gayyaci Dangote Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Kasafin Kudi Mai Sauya Fasali Da Karfafa Rayuwar Al’umma Labarai
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Laraba 11.19.2025 Rediyo
  • Atiku Ya Zargi Gwamnati Da Kama ‘Yan Adawa Labarai
  • Jirage Marasa Matuka Sun Kaiwa Jiragen Ruwan Mai Hari A Gulf Afrika
  • Iran Zata Mayarwa Amurka Martani Amurka
  • Gombe: ‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Ƙungiyar Masu Fashi Da Damfara Ta Yanar Gizo Afrika
  • FIFA, Ta Raba Jaddawalin Rukuni Na Gasar Kofin Duniya 2026. Wasanni
  • Gwamnatin Tarayya Na Kokarin Hana Demokraɗiyya A Najeriya Siyasa
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.