Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Kawayen Amurka Bazasu Shiga Matakin Shugaba Trump Ba
Published: April 14, 2026 at 8:24 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jiya Litinin, Kawayen Amurka a Kungiyar tsaro ta NATO, sunce ba za su shiga cikin matakin Shugaba Trump na killace tashoshin ruwan Iran ba, suna masu shawarar cewa, za su shiga cikin lamarin ne da zarar an daina yaki, matakin da babu mamaki zai fusata shugaba Trump, kuma ya kara bata dangantaka tsakanin kasashe da suke cikin kungiyar.

Trump yace sojojin Amurka za su gama da duk wani jirgin ruwan Iran da ya je kusa da inda Amurka ta shata layi cikin ruwa wadda ya fara aiki daga jiya Litinin, bayanda zaman sulhu da suka gudanar a karshen mako a Pakistan ya kasa cimma matsaya domin kawo karshen yakin na mako shida da Iran.

Tunda farko Trump ya fada cewa Amurka zata yi aiki da wasu kasashe domin su hana zirga zirga a mashigin ruwa na Hormuz, amma daga bisani rundunar sojin Amurka ta kara bada bayanin cewa hana zirga zirga zata shafi jiragen ruwa da suka fito ko za su tashoshin ruwan Iran ne mataki zai shafa.

Amma kawayen Amurkan ciki harda Britaniya da Faransa sunce babu yadda za’ayi su shiga cikin rikicin, maimakon haka suka ce suna aiki kan wasu matakai domin ganin an bude mashigin ruwan, inda ta nan ne kashi 20 cikin dari na mai da iskar Gas da duniya ta dogara akai suke bi.

Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Dakarun Tsaron Ruwan Amurka Sunfara Killace Hanyoyi
Next Post: Papa Roma Leo Yace Zai Cigaba Da Sukan Yake Yake

Karin Labarai Masu Alaka

Guinea Bissau Ta Tsaida Gwaje-Gwajen Allurar Rigakafin Shawara A Kasar Labarai
Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika
JEI Da Abokan Hulɗar Sun Gudanar Da Aikin Shuka Itatuwa Domin Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya Afrika
Shugaban Ukraine Ya Tattauna Da Trump Akan Zaman Lafiya Amurka
Jami’ar ABU Zaria Ta Karbi Kudade Naira Bilyan 1.3 Daga Shirin Nelfund Afrika
‘Yan Sandan Gombe Sun Fara Kama Motocin Da Ba Su Da Lambar Rajista ko Masu Boye Lambobinsu Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Amurka Zata Bada Gudunwa Ga Masu Zanga-Zanga A Iran Sauran Duniya
  • Sanatan Nasarawa Ta Arewa Ya Rasu A Kasar India Najeriya
  • Kasar Colombia Tare Da Amurka Zasu Fitar Da Man Venezuela Labarai
  • Shugaba Trump Ya Kara Matsin Lamba Kan Iran Amurka
  • Jagoran Addinin Kirista A Kaduna Ya Rabawa Fiye Da Musulmai Dubu Kayan Abincin Azumi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Togo Ta Kama Tsohon Shugaban Kasar Burkina Faso Saboda Kitsa Juyin Mulki Afrika
  • Gwamna Inuwa Yahaya Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Ma’aikatan Jiha da Kwamishinoni 23 Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Kasafin Kuɗin 2026 Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.