Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Masar Tayi Yarjejeniyar Makamashi Da Kasashen Norway Da China
Published: January 12, 2026 at 9:03 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gidan telebijin na Masar yace kasar ta rattaba hannu a kan yarjejeniyoyi na kudi dala miliyan dubu daya da dari takwas na samar da makamashi ta hanyoyin da ake iya sabuntawa.

Daga cikinsu har da wasu takardun kwantaraki da wani kamfanin kasar Norway mai suna SCATEC da kuma kamfanin Sungrow na kasar China.

Masar tana fatan samar da kashi 42 cikin 100 na wutar lantarkinta ta makamashin da ake iya sabuntawa nan da shekarar 2030.

Kamfanin SCATEC zai gudanar da aikin farko na kafa tashar samar da wutar lantarki daga hasken rana tare da tashoshin adana wutar lantarkin a Minya dake arewacin Masar kuma wannan tasha zata iya samar da Gigawatt 1.7 na wutar lantarki, inda za a yi amfani da baturan tara wuta da zasu iya tara gigawatt 4.

Aiki na biyu shine wanda kamfanin Sungrow na China zai yi na gina masana’antar kera baturan adana wutar lantarki a yankin Suez.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Kamfanin Jiragen Saman Ethiopia Zai Kafa Babban Filin Jirgi
Next Post: Shugaba Trump Ya Hana Kaiwa Cuba Man Fetur Daga Venezuela

Karin Labarai Masu Alaka

Taron Masu Mu’amala Da Kafar Facebook A Kano Afrika
Jam’iyyu Shida Sun Shiga Zaben Kananan Hukumomin Gombe – GOSIEC Afrika
Guterres: Babban Kuskure Ne Yadda Isra’ila Ta Kai Farmaki A Gaza Labarai
Papa Roma Leo Yace Zai Cigaba Da Sukan Yake Yake Afrika
Hukumar Tsaron Teku A Libya Tafara Janye Jirgi Mai Dauke Da Iskar Gas Labarai
Anyi Jana’izar Mahaifiyar Nasiru El Rufai A Abuja Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ga Dukkan Alamu Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Bai Kare Ba Sauran Duniya
  • Tinubu Ya Sayi Fom Din Takarar Shugaban Kasa Afrika
  • Dalibin Jami’a Ya Rasa Ransa A Birnin Dakar Yayin Zanga Zanga Afrika
  • ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji A Kauyen Wanka Jihar Filato Afrika
  • Ma’aikatan Tattara Kudin Haraji Sunyi Rikici Da Masu Babura A Bauchi Najeriya
  • Ghana Ta Haramta Hakar Ma’adinai A Gandunan Dajin Data Kebe, Labarai
  • Kasar Kenya Zata Samar Da Makamashi Labarai
  • Hukumar Zabe Ta Saukaka Gudanar Da Rijistar Katin Zabe A Najeriya Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.