Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Gidauniyar Sultan Ta Jaddada Muhimmancin Kula Da Lafiyar Yara A Gombe
Published: September 3, 2026 at 4:29 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Masarautar Kaltungo a jihar Gombe dake arewa maso Gabashin Najeriya ta karɓi baƙuncin wani taron yini ɗaya na daidaita ayyukan kiwon lafiya, wanda Gidauniyar Sultan Foundation for Peace and Development ta shirya tare da haɗin gwiwar Hukumar Bunƙasa Kula da Lafiya Matakin Farko ta jihar Gombe.

Taron, wanda ya haɗa sabbin jami’an da aka ɗauka daga masarautu da ƙananan hukumomi tare da sauran masu ruwa da tsaki, ya mayar da hankali ne kan ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙara shigar al’umma wajen aiwatar da shirye-shiryen kiwon lafiya, musamman na yara da mata.

Da yake buɗe taron, Mai Kaltungo, Injiniya Saleh Muhammad, ya buƙaci mahalarta su kasance masu kyautatawa, sauraro da kuma mai da hankali, tare da nuna jajircewa wajen ganin an cimma manufofin shirin.

Mai martaban ya kuma waiwayi tarihin yadda sarakunan gargajiya suka taka muhimmiyar rawa a harkokin kiwon lafiya a Najeriya, yana mai cewa masarautun gargajiya na da muhimmiyar gudunmawa wajen wayar da kan jama’a da tallafa wa shirye-shiryen gwamnati na inganta kiwon lafiya.

A nasa ɓangaren, Babban Jami’in Ayyuka na Sultan Foundation, Barrister Haruna Yusuf, ya jaddada muhimmancin kula da yara da samar musu da abinci mai gina jiki domin inganta lafiyarsu da bunƙasa rayuwarsu.

Barrister Yusuf ya kuma yaba da ƙoƙarin sarakunan gargajiya, ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen inganta lafiyar yara, iyaye mata da sauran al’umma.

Shi ma Dr. Kassim Muhammad ya jaddada muhimmancin allurar rigakafi wajen kare al’umma daga cututtuka, tare da bayyana muhimmiyar rawar da sabbin jami’an da aka ɗauka za su taka wajen sa ido da tabbatar da dorewar ayyukan rigakafi a faɗin Jihar Gombe.

Ya yi kira da a ƙara wayar da kan jama’a domin su fahimci cewa allurar rigakafi ba ta da illa, yana mai cewa rashin yi wa yara rigakafi a lokacin ƙuruciya na iya haifar da matsaloli ga lafiyarsu a nan gaba.

Taron ya kuma samu halartar masu ruwa da tsaki, inda mahalarta suka gabatar da tambayoyi tare da samun amsoshi da ƙarin haske daga masu jawabi kan batutuwan da suka shafi rigakafi, abinci mai gina jiki da sauran muhimman harkokin kiwon lafiya.

Afrika, Kiwon Lafiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: FIFA Ta Ba Da Goyon Bayanta Ga Gyaran Ƙwallon Ƙafa A Najeriya, Shehu Dikko Ya Gana Da Infantino
Next Post: Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Sarakunan Gumel Da Zurmi

Karin Labarai Masu Alaka

Wata Mace Ta Mutu A Hannun ‘Yan-Fashin Daji, Wata Ta Haihu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Rundunar Tsaron Haɗin Gwiwa Ta Arewa Maso Gabas Ta Kashe Fiye Da ‘Yan Ta’adda 438 Labarai
Ƙarin Albashi Zai Fara Aiki Ga Sojojin Najeriya Daga Satumba Afrika
Pads To Prosperity: NEDC Ta Horar Da Mata 280 Kan Kera Pads A Gombe Afrika
Dalibai Sun Koma Makarantu A Wasu Jihohin Najeriya Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rundunan  ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Ta Miƙa Miyagun Ƙwayoyi Da Ta Kama Wa NDLEA. Labarai
  • Atiku Ya Zargi Gwamnati Da Kama ‘Yan Adawa Labarai
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas Najeriya
  • Taron Masu Mu’amala Da Kafar Facebook A Kano Afrika
  • Hari Akan Wata Mashaya Ya Rutsa Da Mutane 9 A Afirka Ta Kudu Afrika
  • Tattalin Arzikin Kasar Uganda Zai Bunkasa A Wannan Shekarar Labarai
  • Shugaba Tinubu ya mika sunayen Sabbin Shugabannin NMDPRA da NUPRC Bayan Murabus Din Farouk Ahmad Da Gbenga Komolafe Najeriya
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Shugaban Makaman Nukiliya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.