Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Shugaba Tinubu Ya Shiga Takara Wa’adi Na Biyu
Published: May 7, 2026 at 7:45 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ranar Alhamis 7 ga watan Mayu ne, Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya kaddamar da neman takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a hukumance ga uwar jam’iyyar APC ta kasa.

A wani gagarumin taro da aka gudanar a dakin taro na *Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre* Mataimakin ya jagoranci mambobin jam’iyyar da suka hada da gwamnoni, da yan majalisun tarayya, da sauran masu madafun iko na da da na yanzu, inda ya miƙa fom din neman takarar ga Shugabannin jam’iyyar a wani mataki na nuna goyon bayan masu madafun iko ga kudurin sake zaben shugaba Tinubu zango na biyu.

Da yake jawabi jim kadan bayan mika fom din, Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya bayyana shugaban a matsayin jagora mai juriya wanda ya yi nasarar Jan ragamar Najeriya zuwa tudun-mun tsira a yayinda guguwar matsalolin tattalin arziki ta so yin awon gaba da ita. Kashim ya kafa hujja da ajandar “Renewed Hope” a matsayin babban dalilin cancantar Shugaba Tinubu ga zagaye na biyu inda ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatin ta kawo sun fara samar da sakamako mai kyau, duk da tsaurin da suka zo da shi a karon farko.

“Kalubalen shekarun da suka gabata ba su raunana Shugaba Tinubu ba; maimakon haka ma sai kara masa kwarewa da suka yi,” in ji Shettima, inda ya ci gaba da cewa

“Wannan gwarzantaka da kwarewa da ya kara ne ya sa mu ke fatan kara masa wata dama”

A nata bangaren, uwar jam’iyyar ta kasa ta nuna cikakken goyon bayanta ga takarar, inda

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda wanda ya karbi takardun takarar, ya ce ayyukan shugaba Tinubu a sassa daban-daban na farfado da kasar sun sa sake zaben nasa ya zama dole.

Yilwatda ya yi nuni da kyautatuwar tattalin arziki da karuwar kwarin gwiwar kasashen duniya ga makomar Najeriya a matsayin hujjojin da jam’iyyar ta dogara da su wajen amincewa da takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Shi ma shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Tajudeen Abbas ya yaba da garambawul din na shugaban Tinubu, wanda ya bayyana a matsayin harsashin farfadowar kasa mai dorewa.

Ita ma kungiyar Gwamnonin APC ta bakin Shugabanta kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma wanda gwamnoni 12 suka rufa wa baya ta nuna goyon baya na bai-daya ga takarar

Gwamnonin da suka halarci taron su ne na jihohin Plateau, Ogun, Niger, Kaduna, Ondo, Katsina, Borno, Cross River, Taraba, Yobe, Nasarawa, da Bayelsa.

A yanzu dai mika tikitin takarar a hukumance ya kawo karshen rade-raden da ake yi game da aniyar shugaban ta neman wa’adin Mulki na biyu kamar yadda ta bayyana irin hadin kan Shugabanni na bai daya da ake dakon gani a zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC.

Shugabannin jam’iyyar sun yi kira ga mambobinsu da su fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu don “kare fatan Najeriya.”.

Afrika, Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Hukumar NAHCON Ta Bude Asibiti A Madina
Next Post: Ana Kokarin Kawo Karshen Matsalar Kashe Matafiya A Filato

Karin Labarai Masu Alaka

Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau Ya Koma Jam’iyyar APC Afrika
Kasashen Amurka Da China Sun Matsawa Ghana Domin Rage Kudaden Haraji Afrika
‘Yan Sanda A Finland Sun Kwace Jirgin Ruwan Kasar Rasha Afrika
Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa Afrika
Kasar Habasha Ta Cimma Matsaya Da Masu Binta Bashi Afrika
Anyi Rashin Mutane Da Yawa Yayinda Bom Ya Fashe Ana Sallar Magariba Maiduguri Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Masoya Kungiyar Kwallon Kafar Morocco Suna Cikin Farin Ciki Bisa Hukuncin Kotu Afrika
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Juma’a 11.21.2025 Rediyo
  • Isra’ila Ta Cire Sunayen Wasu Mutane Biyu Cikin Wadanda Take Fako Afrika
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Nada Sabon Ministan Kudi Labarai
  • Idan Allah Yasa Muka Kafa Gwamnati Zamu Kyautata Wa Ma’aikata Yakubu Adamu Dan Takarar Kujeran Gwamnan Bauchi Labarai
  • Magoya Bayan Obi Sun Yi Tutsu Gabanin Zaben 2027 Siyasa
  • Tinubu Ya Bayyana ‘Yan Bindiga Da Cewa Ruwa Yakarewa Dan Kada Afrika
  • ‘Yan Sanda A Tsibirin Bahamas Sun kama Mijin Wata Ba Amurkiya Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.