Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamnatin Najeriya Tace A Maboyar ‘Yan Ta’adda Aka Kai Harin Jilli
Published: April 14, 2026 at 8:36 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi karin haske kan harin nan da jiragen yakin Rundunar Sojin Sama ta Kasa (NAF) suka kai a yankin Jilli na Karamar Hukumar Gubio, Jihar Borno, ranar 11 ga Afrilu, 2026.

Gwamnati ta bayyana cewa harin ba na kan-mai-uwa da wabi ba ne; an kai shi ne kai-tsaye kan maboyar ’yan ta’adda.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a a Najeriya Mohammed Idris ya jaddada cewa harin na karkashin Operation HADIN KAI ne, kuma an gudanar da shi ne bayan samun kwararan hujjoji na sirri.

Wannan yanki na Jilli, wanda aka fi sani da Kasu Daulaye (Kasuwar ’yan ta’adda), ya dade yana karkashin ikon mayakan Boko Haram da ISWAP. A nan ne suke Karbar haraji a hannun jama’a, Siyan kayayyakin bukata, da Shirya yadda za su kaddamar da hare-hare.

Sanarwar ta kara da cewa, a ranar 12 ga Afrilu, sojoji sun kama wani matashi mai shekara 15 mai suna Tijjani a yankin Ngamdu. Tijjani ya amsa cewa shi ne yake kai wa ’yan ta’addan ISWAP kudi da sauran kayayyaki a tsakanin Jilli da wasu wurare, lamarin da ya nuna yadda mahukuntan ke amfani da kananan yara wajen aikata barna.

Haka zalika, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya tabbatar da cewa tun shekaru biyar da suka gabata aka rufe kasuwannin Jilli da Gazabure saboda yadda ’yan ta’adda suka mamaye su.

Duk da cewa gwamnati ta kare matakin sojoji, ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa. Ministan ya bayyana cewa:

“Rayuwar kowane dan Najeriya tana da muhimmanci, kuma muna matukar da na sani kan asarar rayukan farar hula da aka samu.”

Domin tabbatar da gaskiya da adalci, Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin gudanar da bincike mai zaman kansa kan yadda aka tsara harin da kuma inda aka samu kuskure.

A yanzu haka, gwamnati tana hada gwiwa da hukumomin agaji na NEMA da SEMA domin kai dauki ga iyalai da wadanda suka jikkata a jihohin Borno da Yobe.

Gwamnati ta bukaci fararen hula da su kiyaye shiga yankunan da aka sanya wa takunkumi, su kuma ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai domin kawo karshen wannan fitina.

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Za A Cigaba Da Tattaunawa Domin Kawo Karshen Yakin Gabas Ta Tsakiya
Next Post: Jiragen Ruwa Suna Biyayya Ga Dokar Hana Ketare Ruwa

Karin Labarai Masu Alaka

Shugabannin Kiristocin Arewa Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Ummulkhairi Afrika
Za’a Fuskanci Bala’in Yunwa A Najeriya Labarai
Masu Luwadi Na Fuskantar Tara Da Daurin Shekaru 20 A Nijar Afrika
Ga Fili Ga Doki Najeriya
Masar Ta Kayyade Farashin Buradi A Kasar Afrika
Gwamnan Jihar Adamawa Fintiri Ya Koma APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Anyi Rashin ‘Yan Jarida 6 A Jihar Gombe Sakamakon Hatsarin Mota Labarai
  • Amurka Na Shirin Kauracewa Taron Kungiyar Kasashen G20 Afrika
  • Kasashe Biyar Zasu Tura Sojoji Domin Ayyukan Wanzar Da Zaman Lafiya A Gaza Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sama da mutane dubu 500 ne yanbindiga suka kora daga gidajensu a Jihar Nejan Najeriya. Najeriya
  • Chadi Ta Sauyawa ‘Yan Gudun Hijira Matsuguni Afrika
  • Akalla Mutane 8 Sun Mutu Biyo Bayan Bindiga Da Wata Tanka Tayi Afrika
  • Za A Rantsar Da Mainasara Kogo A Matsayin Shugaban Kundin Da’ar Ma’aikata Labarai
  • Farashin Zinari Yayi Tashin Gwauron Zabi Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.