Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Rundunar Sojin Najeriya Ta Kubutar Da Wasu Mutane 31 Da Aka Yi Garkuwa Dasu
Published: April 6, 2026 at 7:24 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana a jiya Lahadi cewa ta kuɓutar da wasu fararen hula 31 da aka yi garkuwa da su, inda aka kai wani hari a wata coci a Arewa maso yammacin jihar Kaduna, An kuma gano gawar mutane biyar a wurin da lamarin ya faru.

Sojin sun ce harin ya faru ne a lokacin gudanar da ibadar Easter a cocin da ke ƙauyen Ariko, a ƙaramar hukumar Kachia. Sun ƙara da cewa dakarun soji na bin sawun maharan.

Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta (CAN) reshen jihar Kaduna, Caleb Maaji, ya ce an kai hare-hare kan majami’u biyu a ƙauyen Ariko a ranar Lahadi. Ya ƙara da cewa mutane bakwai sun mutu, yayin da adadin waɗanda aka yi garkuwa da su bai kai ga tabbatarwa ba. “Ana ci gaba da tattara bayanai,” in ji Maaji ga kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Arewacin Najeriya na fuskantar matsalar tashin hankali tsawon shekaru, ciki har da sace mutane da nufin neman kuɗin fansa da kuma hare-haren kauyuka, inda ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke aiki daga manyan dazuzzuka a yankin.

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Kungiyar HPV A Jihar Gombe Ta Jagoranci Yaki Da Karuwar Cutar Daji
Next Post: Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Zata Karbi ‘Yan Gudun Hijirar Da Amurka Ta kora

Karin Labarai Masu Alaka

Isra’ila Tace Bazata Sake Kai Hari Kan Cibiyar Gas Ta Iran Ba Afrika
Ma’aikatar Tsaron Amurka Zata Kara Samar Da Makamai Amurka
Amurka Zata Aika Jiragen Yaki Biyu Gabas Ta Tsakiya Amurka
‘Yan Bindiga Sun Jikkata Mutane A Arewacin Kasar Benin Afrika
Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Wasu Muhimman Abubuwa Da Najeriya Ba Zata Manta Da Su Ba A 2025 Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Gombe Ta Yi Fice A Duniya: Maryam Dan’azumi Ta Lashe Gasar Alƙur’ani Na Ƙasa Da Ƙasa Afrika
  • Tsohuwar Ministan Albarkatun Mai Ta Bayyana A Kotu Najeriya
  • Habasha Tafara Gina Filin Jirgin Sama Mafi Girma A Afirka Afrika
  • Sojin Najeriya Da ‘Yan Ta’adda Sunyi Taho Mugama Najeriya
  • Gwamnatin Jihar Filato Ta Sauke Hakimin Mushere Afrika
  • Rundunar Operation Endurance Peace Ta Gano Wajen Kera Makamai A Jihar Filato Afrika
  • Abba Kabir Yusuf Ya Koma Jam’iyar APC Siyasa
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.