Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya Tayi Kakkausar Lafazi Game Da Harin Maiduguri
Published: March 17, 2026 at 10:36 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya, karkashin jagorancin Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ta yi Ala-wadai da harin bama-bamai da ya auku a birnin Maiduguri na jihar Borno, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da jikkatar mutane da dama.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ta bakin shugaban kungiyar, Inuwa Yahaya, gwamnonin sun bayyana harin a matsayin abin takaici da kuma babbar barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma a yankin Arewa maso Gabas. Sun jajantawa gwamnatin jihar Borno da iyalan wadanda abin ya shafa, tare da addu’ar Allah ya jikansu da rahama, ya kuma bai wa wadanda suka jikkata lafiya.

Kungiyar ta bukaci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen bincike domin gano wadanda ke da hannu a harin, tare da tabbatar da an hukunta su bisa doka.

Haka zalika, sun jaddada bukatar daukar matakan gaggawa domin kawo karshen irin wadannan hare-hare, tare da karfafa tsaro musamman a wuraren taruwar jama’a.

Gwamnonin sun kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara tallafawa rundunonin tsaro da kayan aiki na zamani, da kuma inganta hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da al’umma domin dakile ayyukan ta’addanci a fadin yankin.

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Tinubu, Akpabio da Ministoci 9 Zasu Tafi Ƙasar Birtaniya
Next Post: Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Ranakun Hutun Sallar Azumi

Karin Labarai Masu Alaka

Tsohon Jagoran Masu Kishin Kasa A Hungry Ya Amince Da Shan Kaye Labarai
An Kaddamar Da Jigilar Maniyyata Aikin Hajji A Abuja Afrika
Malaman Addinin Musulunci Da Kirista Sunyi Bikin Cika Shekara 15 Na Iftar A Najeriya Afrika
Akwai Bukatar Hukunci Mai Tsanani Ga Duk Wanda Yayi Fyade Najeriya
Amurka Tafara Yiwa Kasar Iraq Barazana Amurka
Iran: Za A Gudanar Da Jana’izar Khamenei Bayan Kwanaki Goma Na Muharram Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Zuwa Jami’ar Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Jihar Neja Ta Soke Lasisin Mallakar Wasu Manyan Filaye A Jihar Labarai
  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai Wasanni
  • Tinubu Ya Yi Allah Wadai Da Kashe-kashen Jos Da Kaduna Afrika
  • Kotun Amurka Ta Soke Harajin Fito Da Shugaba Trump Ya Kakabawa Kayan Kasashen Waje Amurka
  • Ukraine Ta Mika Wa Amurka Daftarin Yarjejeniya Da Rasha Sauran Duniya
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Cin Karensu Babu Babbaka A Najeriya Afrika
  • PDP Ta Koka Kan Rushe-rushe, Korar Gombawa Motors da Zaɓen Kananan Hukumomi A Gombe Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.