Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Tsohuwar Jarumar Kannywood Wasila Ismail Ta Rasu Afrika
  • Za’a Fassara Hudubar Arfa Da Harshen Hausa Afrika
  • An Kamallah Jigilar Alhazain Najeriya Domin Hajjin 2026 Afrika
  • Bola Ahmed Tinubu Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Na Shugaban Kasa A Gombe Afrika
  • APC Ta Ayana Tsohon Gwamnan Bauchi M.A Abubakar A Matsayin Dan Takarar Gwamna Afrika

Hukumar ‘Yan Sanda Ta Bukaci Jama’ar Jos Ta Arewa Su Rika Bin Doka
Published: April 4, 2026 at 8:34 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar ‘yan sanda a jihar Filato ta ja kunnen al’ummar yankin Jos ta Arewa kan su tabbatar sun shige gidajen su kafin karfe uku na yamma.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Filato, Alfred Alabo yace jami’an tsaro zasu aiwatar da umurnin da gwamnatin jihar ta bayar na hana fita daga karfe uku na yamma zuwa karfe bakwai na safe, bayan share kwanaki biyu da al’ummar yankin suka yi a kulle.

Jami’in ‘yan sandan yace duk wanda aka kama a titi kan kowani dalili, hukuma zata kama shi ya fuskanci hukunci.

Alfred Alabo ya kuma ce sun tattauna da shugaban jami’ar Jos, Farfesa Tanko Ishaya don neman hanyoyin kai dalibai dake bukatar komawa gidajensu zuwa garuruwansu.

Kakakin ‘yan sandan na jihar Filato yace basa son hankalin daliban ya tashi, shi ya sa kwamishinan ‘yan sanda a jihar ya bada umurnin a samarda tsaro a gidajen kwanan daliban da ma harabar jami’ar baki daya.

Rikicin a ranar Laraba ya sake barkewa a cikin garin Jos, bayan gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana fita na kwanaki biyu da ta sanya a karamar hukumar Jos ta Arewa.

Duk da shike lamarin ya lafa, bayanai na nuni da cewa rayuka sun hallaka, wassu sun sami raunuka, yayinda ‘yan kasuwa suka rurrufe hajjarsu suka gudu.

Sheikh Farouk Omar, na’ibin limamin masallacin Haibar dake Jos, yace sai gwamnati ta jajirce wajen tabbatar da hukunci kan wadanda ta samu da laifi, shine zai samadda zaman lafiya.

Shima Pharmacist Markus Kanda yace kamata yayi hukumomi su dauki matakan tsaro da zarar ga alamun tashin hankali.

A ranar Alhamis ne ake sa ran shugaban kasa, Bola Tinubu zai kawo ziyarar jaje wa al’ummar jihar Filato, biyo bayan harin da wassu ‘yan bindiga suka kai kan al’ummar jihar a Angwan Rukuba, da ma yamutsin da ya auku a jiya Laraba da yayi sanadin rasa wassu rayuka a wassu sassan garin na Jos.

Daga Jos Ga Rahoton Wakiliyar GTA Hausa Amurka Ke Magana Zainab Babaji

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/04/AUD-20260404-WA0006.mp3
Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Prime Ministar Italiya Ta Ziyarci Saudi Arabia
Next Post: Iran Ta Harbo Jiragen Yakin Amurka Biyu

Karin Labarai Masu Alaka

Sakataren Kungiyar NATO Yayi Magana Da Hukumomin Kasashe Afrika
Kasar China Ta Sauka Daga Ragamar Bada Bashi Labarai
Indonesia Zata Kafafa Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Gaza Labarai
Jami’an Tsaro Suna Farautar Wasu ‘Yan Ta’adda A Najeriya Afrika
Peter Obi Ya Gayyaci Gwamnan Bauchi Bala Abdulkadir Kan Yazo Su Hada Kai Su Gyara Nijeriya. Labarai
Domin Inganta Tsaro Najeriya Ta Sayi Jiragen Yaki A Kasar Italiya Tsaro

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Tsohuwar Jarumar Kannywood Wasila Ismail Ta Rasu
  • Za’a Fassara Hudubar Arfa Da Harshen Hausa
  • An Kamallah Jigilar Alhazain Najeriya Domin Hajjin 2026
  • Bola Ahmed Tinubu Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Na Shugaban Kasa A Gombe
  • APC Ta Ayana Tsohon Gwamnan Bauchi M.A Abubakar A Matsayin Dan Takarar Gwamna

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hukumomin Bada Agaji Sun Fadakar Da Al’ummar Jihar Gombe Afrika
  • Farashin Mai Ya Cigaba Da Tashi Afrika
  • Wakilan Rasha Da Ukraine Sun Tattauna A Abu Dhabi Ranar Juma’a Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Bayan Shafe Shekaru Hudu A Mulki Sarkin Hausawan Ibadan Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Janar Christopher Zai Maye Gurbin Ministan Tsaron Najeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Abun Da Kuke Buƙatar Sani Game Da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka 2025 Wasanni
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika
  • Hukumar Zabe A Najeriya Ta Cigaba Da Rijistar Katin Zabe Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.