Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Gwamnan Bauchi Ya Shiga Neman Mafita Kan Lalacewar Matatar Ruwan Alkaleri
Published: August 30, 2026 at 1:26 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Bauchi a Arewa Maso Gabashin Najeriya Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya gana da Shugaban Kamfanin Hummels Water Engineering na ƙasar Hungary, Injiniya Peter Hummel, a Abuja, domin nemo mafita kan matsalar matatar ruwan Alkaleri.

Ganawar ta biyo bayan bukatar Gwamna Bala Mohammed ga injiniyoyin Hungary da suka girka matatar, da su dawo Jihar Bauchi domin gudanar da gyare-gyare da aikin fasaha da zai ba da damar dawo da matatar cikin cikakken aiki.

Matatar ruwan, wadda gwamnatin Hungary ta gina tare da bai wa Najeriya a matsayin tallafin jin kai a shekarar 2023, tana da ƙarfin samar da kusan lita dubu 40 na tsaftataccen ruwa a kullum, wanda ke amfanar da kimanin mutane dubu 4.

Gwamnan ya bayyana cewa matatar ta daina aiki ne sakamakon matsalolin kula da ita da kuma gudanar da aikinta, inda ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki matakin dawo da injiniyoyin da suka girka ta domin su taimaka wajen gano matsalar tare da magance ta.

Sanata Bala Mohammed ya gode wa gwamnatin Hungary da Kamfanin Hummels Water Engineering bisa haɗin gwiwa, yana mai jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da ingantattun hanyoyin samun tsaftataccen ruwan sha ga al’ummar Jihar Bauchi.

Ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na rage matsalar ƙarancin ruwan sha da inganta rayuwar al’ummomin da ke fama da ƙalubalen samun tsaftataccen ruwa.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sana'o'i, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Shugaba Tinubu Zai Shafe Makonni Uku A Hutun Shekara-Shekara
Next Post: Gwamna Inuwa Yahaya Ya Jaddada Haƙuri Da Fahimtar Juna A Siyasa

Karin Labarai Masu Alaka

Suvr Jahun: Ya Kamata Obasanjo Ya Bar Al’umar Ƙasa Su Fito Da Wadda Suke So 2027 Najeriya
Rasha: Zamu Ba Gwamnatin Venezuel Gudunmawa Sauran Duniya
Jam’iyar APC A Najeriya Ta Kaddamar Da Bada Shaidar Zama Dan Jam’iyyar Ta Na’ura Mai Kwakwalwa Siyasa
Za’a Jima Ana Fama Da Tsadar Farashin Mai Afrika
An Watse A Tattaunawar Tsakanin Rasha Da Ukraine Batare Da Cimma Matsaya Ba Labarai
Kungiyar MDD Ta Bukaci Ayi Bincike Game Da Kashe ‘Yan Iran Sauran Duniya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Farashin Mai Yayi Tashin Gwaron Zabi Afrika
  • Kasashen AES Sun Buɗe Gidan Talabijin Na Bai Daya Afrika
  • Ko Arsenal Zata Iya Lashe Gasar Firimiya lig Na Bana Wasanni
  • Gobara Ta Tashi A Makarantar Koyon Jinyar Dabbobi Dake Jihar Kano Najeriya
  • Gwamnatin Kano Ta Rufe Gidajen Bukukuwa Da Shakatawa Labarai
  • Hukumar Kare Hakkin ‘Yan Jarida Tace Isra’ila Ce Ta Kashe ‘Yan Jarida Kashi Biyu Bisa Uku Labarai
  • Amurka Zatayi Amfani Da Sansanonin Birtaniya Amurka
  • Usman Maiyama Ne Gwarzon Kamun Kifin Argungu Bana Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.