Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari Afrika
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe Afrika
  • Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS Afrika
  • Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Yarjejeniya Da ‘Yan Takara A Gombe Afrika

Iran Ta Kai Hari Matatar Mai A Kuwait
Published: March 20, 2026 at 9:36 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Iran ta kai hari kan wata matatar mai a Kuwait ranar jumma’a, Isra’ila kuma ta kashe kakakin rundunar juyin juya hali na Iran, yayinda ake ganin wannan yaki na hadin guiwar Amurka da Isra’ila kan Iran bai nuna wata alamar kawo karshe ba.

Isra’ila tayi alkawarin ba zata sake kai hari kan cibiyar iskar gas na Iran da ake kira ko yake kudancin Pars, wadda Iran ta dauki fansa kan Qatar, da yayi mummmunar ta’adi da aka ce zai janyo wa duniya karancin iskar Gas da zai dauki shekaru masu yawa.

Yayinda Musulmi a yankin kamar sauran Musulmi suke kokarin sallar idi, na kammala watan azumi, a kuma dai dai da bikin Nowuz, watau sabuwar shekara ga Farisawa, zaton kawo karshen yakin da yake shiga mako na hudu, zuwa yanzu dai ba’a ga alama ba.

Farashin mai da ake kira Brent ya sassauto kadan zuwa dala 108 kan ko wace ganga, bayan da yayi tashin gwaron zabbi ranar Alhamis, saboda faragabar duk cikas da aka samu wajen wadatar makamashi zai yi illa ga tattalin arzikin duniya.

Koda an tsaida yakin nan bada jumawa ba, ba za’a sami waraka cikin gaggawa ba sakamakon fitintinun da suka biyo bayan farmaki daga sama, da kuma rufe mashigin ruwan Hormuz da Iran tayi, wacce itace hanyar da ake bi domin jigilar kashi 20 cikin dari na mai da iskar gas da duniya take amfani dashi.

Kasashen Jamus, da Britaniya, da Faransa, da Italiya, da Netherlands, da japan, ranar Alhamis, a wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar, sunyi alkawarin daukar matakai da suka wajaba na tabbtar da ganin zirga zirga ta tabbata a mshigin ruwan Hormuz, amma wazirin Jamus ko Chancellor Friedrich Merz, yace hakan zai ta’allaka ne idan aka kawo karshen yakin.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, bayan taron koli na kungiyar tarayyar turai tayi a Brussels, yace kare dokokin kasa da kasa, da kuma sassauta rikici shine “gwargwadon abunda zamu iya yi,” ya kara da cewa ban ji wani anan wanda ya bayyana sha’awar shiga wannan rikici ba.

Shugaban Amurka Donald Trump, a ranar jumma’a, ya kira kawayen Amurka da suke cikin Kungiyar tsaro ta NATO, a zaman ragaye, saboda sunki su taimaka a yakin Iran, da suka hada da kasa daukar mataki mafi sauki na tabbatar da mashigin ruwan Hormuz yana bude, amma suna da bakin kukan cewa mai yayi tsada.

Ahalinda ake ciki kuma, Amurka zata tura karin dubban sojojinta na kundun bala zuwa gabas ta tsakiya, kamar yadda wasu majiyoyi uku da suke da masanaiya kan lamarin suka shaidawa kamfanin dilancin labarai na Reuters a ranar Jumma’a. A kuma dai dai lokacin da sabon shugaban addinin Iran ya yaba da hadin kan kasar, da kuma “turjiyar da suke nunawa.”

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: An Tsinto Gawarwakin ‘Yan gudun Hijira A Bakin Tekun Comoros
Next Post: Ukraine Ta Aika Tawagar Kwararru Gabas Ta Tsakiya

Karin Labarai Masu Alaka

Domin Inganta Tsaro Najeriya Ta Sayi Jiragen Yaki A Kasar Italiya Tsaro
Shugaban Ƙasar Djibouti Ya Sake Lashe Zaben Shugaban Kasar Afrika
‘Yan-Ta’adda Sun Yi Ma Wasu Mutane Yankan Rago A Jihar Neja Labarai
Majalisar Tarayya Ta Amince Da Gyara Dokar Kasafin Kudi Labarai
Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Lumbala Shekaru 30 Bisa Laifin Cin Zarafi Labarai
Samar Da Albarkatun Mai Ya Ragu A Iraq Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe
  • Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS
  • Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Yarjejeniya Da ‘Yan Takara A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Afrika
  • Tinubu Yafara Wasu Dabaru Domin Samun Kuri’u Siyasa
  • Hukumar ‘Yan Sanda Ta Bukaci Jama’ar Jos Ta Arewa Su Rika Bin Doka Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Kasafin Kuɗin 2026 Najeriya
  • Nijar: Zamu Tsananta Bincike A Bakin Iyakokin Mu Afrika
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Shugaban Makaman Nukiliya Afrika
  • Sanata Barau Ya Raba Motoci Da Babura Ga Al’ummar Kano Ta Arewa Afrika
  • Sojoji Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda a Kukareta Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.