Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • NALV Da NEDC Sun Kaddamar Da Horon Makonni Biyu Ga Malaman Tsangaya Da Islamiyya Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa, Ya Nemi Haɗin Kai Afrika
  • Kotu Ta Dawo Shari’ar Tsohon Minista Sirika Labarai
  • Hukumar Tsaron Muhimman Kadarorin Najeriya Ta Nemi Haɗin Gwiwar NUJ Wajen Yaƙi da Labaran Ƙarya Afrika
  • An Sanya Hannu kan Yarjejeniyar Ci Gaba Tsakanin Kamfanin Ashaka Da Maiganga Labarai

Gwamnatin Kano Zata Dauki Mataki Game Da Kisan Dorayi
Published: January 20, 2026 at 7:52 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta jagoranci shigar da ƙara kan kisan gillar da aka yi wa wata matar aure da ƴ aƴanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke birnin Kano, lamarin da ya jefa al’ummar jihar cikin alhini da girgiza.

Gwamnatin ta bayyana kisan a matsayin mummunan aiki na rashin tausayi da rashin imani wanda ya girgiza zukatan al’ummar jihar tare da zama babban cin zarafi ga bil’adama da doka.

A cikin wata sanarwa da babban lauyan jihar kuma kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN ya ce bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf, gwamnatin jihar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da daukacin al’ummar Kano.

”Gwamnati na tare da iyalan da abin ya shafa, tare da tabbatar musu da cewa ba za a barsu su kaɗai ba a wannan mawuyacin lokaci,” in ji sanarwar.

Gwamnatin ta yaba wa rundunar ƴansandan jihar bisa gaggawar ɗaukar matakin bincike da ya kai ga kama manyan waɗanda ake zargi da aikata laifin.

A cewar sanarwar, wannan mataki na nuna ƙudirin hukumomin tsaro na tunkarar aikata laifuka da dawo da amincewar jama’a ga tsaro da adalci.

Gwamnatin ta jaddada cewa za a gudanar da shari’ar cikin gaggawa da ƙwarewa ta hannun Ofishin Babban Lauyan jihar, inda za a kafa tawagar lauyoyi ta musamman domin tabbatar da adalci.

Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Gana Da Shugaba Tinubu
Next Post: Talauci Ya Ragu A Tsakanin Al’ummar Jihar Jigawa

Karin Labarai Masu Alaka

Mutane 13 Sun Mutu Inda Wasu 57 Suka Jikkata A Barundi Afrika
Sojin Israela Sunkai Hari Kan Falatsinawa Tsaro
‘Yan Kasashen Afirka Da Dama Suna Fafatawa Da Rasha A Yaki Da Ukraine Afrika
Shugaba Trump Ya Kara Matsin Lamba Kan Iran Amurka
Isra’ila Ta Kashe Babban Jami’in Tsaron Iran Ali Larjani Afrika
Sojojin Isra’ila Sun Kashe Babban Kwamandan Kungiyar Hezbollah Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • NALV Da NEDC Sun Kaddamar Da Horon Makonni Biyu Ga Malaman Tsangaya Da Islamiyya
  • Shugaba Tinubu Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa, Ya Nemi Haɗin Kai
  • Kotu Ta Dawo Shari’ar Tsohon Minista Sirika
  • Hukumar Tsaron Muhimman Kadarorin Najeriya Ta Nemi Haɗin Gwiwar NUJ Wajen Yaƙi da Labaran Ƙarya
  • Lauyoyin Pantami Sun Ƙalubalanci Rashin Sunansa, Sun Bada Sa’o’i 72

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaban Hukumar NAHCON Ya Ajeye Mukaminsa Labarai
  • Shugaba Trump Yace Amurka Takai Hari Kharg Tsibiri a Kasar Iran Afrika
  • Maulidin 2026: IMC Ta Yi Kira Da Ƙarfafa Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Najeriya Afrika
  • Shugaban Kasar Brazil: Yakamata Amurka Ta Gurfanar Da Shugaban Venezuela A Kotu Afrika
  • GOSEMA Ta Horar Da Mambobin LEMCs A Jihar Gombe Afrika
  • Da Arzikin Mu: Bamu Ba Bautawa Turawan Yamma Afrika
  • Birtaniya Zata Fara Raba Rigakafin Allurar Cutar Sankara Kimiya
  • Kasar Uganda Ta Tsare ‘Yan Jam’iyyun Adawa Dubu Biyu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.