Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Talauci Ya Ragu A Tsakanin Al’ummar Jihar Jigawa
Published: January 20, 2026 at 7:59 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana cewa ta samu raguwar matakin talauci da kashi 15 cikin 100 a fadin jihar, sakamakon matakan bunkasa tattalin arziki da ta dauka a baya-bayan nan.

Gwamnatin ta ce wannan nasara na nuna yadda shirye shiryenta ke fara haifar da da mai ido.

Gidan Rediyon jihar Jigawa ya rawaito cewa Gwamnan jihar, Dakta Umar Namadi, ne ya bayyana hakan a Birnin Kudu yayin bude babban kantin sayar da kayayyaki mai suna Akilu Aliyu Multipurpose Shopping Complex. Gwamnan ya ce wani rahoton bincike da aka kammala a watan Satumba na shekarar da ta gabata ne ya nuna raguwar talauci a jihar.

Gwamna Umar Namadi ya kara da cewa gwamnatin jihar ta tallafa wa kimanin mutane dubu 400 ta hanyar shirye-shiryen samar da ayyukan yi, yayin da kananan da matsakaitan ’yan kasuwa kusan dubu 230 suka amfana da rancen kudi daga Bankin Raya Masana’antu domin bunkasa harkokinsu.

Ya jaddada cewa gwamnatin Jigawa za ta ci gaba da bai wa kungiyoyi da daidaikun mutane goyon baya domin kara samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin jihar.

Siyasa

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Kano Zata Dauki Mataki Game Da Kisan Dorayi
Next Post: Fadar Sarkin Musulmi: Talata Ne 1 Ga Watan Sha’aban Na 1447AH

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
Kasar Zimbabwe Ta Samar Da Dokar Tsawaita Mulkin Mnangagwa Zuwa 2030 Labarai
Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yayi Murabus Afrika
Mutane Biyu Sun Mutu A Yayin Zaben Shugabannin Gundumomin APC A Jihar Ondo Najeriya
Shugaban Amurka Yayi Watsi Da Tattaunawar Kawo Karshen Yaki Da Iran Afrika
Zabebben Shugaban Hungary Yace Zaidawo Da Tsarin Dimokraɗiyya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ana Cigaba Da Yaki Tsakanin Amurka Da Isra’ila Da Kasar Iran Afrika
  • Rikicin Siyasa A Jihar Rivers Sakamakon Ayyana Fubara A Matsayin Shugaban APC Siyasa
  • ECOWAS Da AU Sun Nuna Damuwa Kan Juyin Mulki A Guinea-Bissau Afrika
  • Gwamna Inuwa Yahaya Ya Bukaci Al’ummar Gombe Su Haɗa Kai Wajen Yaƙi Da Ta’addanci Afrika
  • Masu Luwadi Na Fuskantar Tara Da Daurin Shekaru 20 A Nijar Afrika
  • ‘Yan Tawayen M23 Masu Samun Goyon Bayan Rwanda Basu Jamye A Ulvira Ba Labarai
  • Gwamnatin Tarayya Ta Ce Babu Musguna Wa ’Yan Jarida A Mulkin Tinubu Labarai
  • Gwamna Inuwa Yahaya Ya Amince Da Gyaran Fadar Sarkin Gombe Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.