Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Jam’iyyar APC Ta Ayana Jamilu Gwamna A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Gombe
Published: May 21, 2026 at 6:21 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jam’iyyar APC a jihar Gombe ta ayana Dakta Jamilu Isiyaku Gwamna a matsayin ɗan takararta na gwamna domin babban zaɓen shekarar 2027, bayan nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar.

Sakamakon zaɓen da kwamitin gudanarwa ya sanar ya nuna cewa Dakta Jamilu Gwamna ya samu ƙuri’u 247,161, inda ya kayar da sauran ‘yan takarar biyu da suka fafata a zaɓen.

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya samu ƙuri’u 12,120, yayin da tsohon Ministan Sufuri, Sanata Said Ahmed Alkali, ya samu ƙuri’u 11,612.

Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna, Sanata Sani Danladi, ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana tare da bin ƙa’idojin jam’iyyar da tanade-tanaden dokar zaɓe.

Ya kuma yaba wa mambobin jam’iyyar APC a faɗin jihar bisa yadda suka fito domin kaɗa ƙuri’a cikin tsari da lumana, yana mai cewa hakan alama ce ta haɗin kai da ƙarfin jam’iyyar a jihar Gombe.

An sanar da sakamakon ne a sakatariyar jam’iyyar APC da ke Gombe, a gaban jami’an hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, masu sa ido kan zaɓe, jami’an tsaro, kafafen yaɗa labarai da kuma manyan jami’an jam’iyyar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Najeriya Da Poland Za Su Hada Kai Kan Tsaro da Bunƙasa Tattalin Arziki
Next Post: Gwamnatin Najeriya Ta Karyata Raɗe-Raɗin Canza Sunan Kasar Da Soke Shari’a A Arewa

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yansandan Uganda Sun Tsare ‘Yar Fafutukar Kare Hakkin Bil’adama Sarah Bireete Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kasar India Ta Sayi Iskar Gas Daga Iran Labarai
Mutane 27 Sun Rasa Rayukan Su A Najeriya Afrika
Shugaba Trump Ya Kara Matsin Lamba Kan Iran Amurka
Rasha: Zamu Ba Gwamnatin Venezuel Gudunmawa Sauran Duniya
Najeriya Da Maroko Sun Kulla Yarjejeniya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Amurka Ta Kai ‘Yan Cirani Kamaru Afrika
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Gabatar Da Kudi Fiye Da Naira Triliyan 58 A Matsayin Kasafin 2026 Najeriya
  • Gabannin Harin Amurka Da Isra’ila Iran Farisa Ta Shirya Nata Afrika
  • Hukumomin Kasar China Suna Goyon Bayan Somaliya Labarai
  • Dillalan Mai Suna Fuskantar Karancin Mai Sakamakon Yakin Amurka Da Iran Afrika
  • ‘Yan Uwan Wadanda Aka Kashe Sunkai Kara Kotu Amurka
  • Sojoji Sun Murkushe ‘Yan Bindiga A Jihar Sakkwato Labarai
  • Malami: Gwamnatin APC Ta Gaza – “Yan-Kasa Kuwa Na Da Katin Zabe” Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.