Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Tinubu Ya Sayi Fom Din Takarar Shugaban Kasa
Published: April 28, 2026 at 2:28 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Ikeja a jihar Legas, James Faleke, ya karɓi fom ɗin na gani Ina so da na tsayawa takara na jam’iyyar APC a madadin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Majiyoyi sun rawaito cewa, sakataren tsare-tsare na ƙasa na APC, Suleiman Argungu, ne ya bayyana fara wannan tsari na siyar da fom a ranar Talata a Abuja, inda ya miƙa fom ɗin ga Faleke, wanda kuma shi ne wanda ya kafa ƙungiyoyin goyon bayan Tinubu.

Rahotanni sun nuna cewa Faleke ya biya kuɗin fom ɗin da ya kai naira miliyan 100 a madadin shugaban ƙasar, abin da ke nuna fara shirye-shiryen neman sake zaɓen Tinubu a hukumance.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta tsara gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar tarayya a ranar Asabar, 16 ga Janairu, 2027, yayin da zaɓen gwamna da na majalisun jihohi za su gudana a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.

Haka kuma, hukumar ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyun siyasa daga ranar 23 ga Afrilu, 2026 zuwa 30 ga Mayu, 2026, tare da warware duk wata takaddama da ka iya tasowa a wannan lokaci.

INEC ta kuma bayyana cewa yaƙin neman zaɓe na shugabancin ƙasa da na majalisar tarayya zai fara ne daga ranar 19 ga Agusta, 2026, yayin da na gwamna da na majalisun jihohi zai fara daga ranar 9 ga Satumba, 2026.

Ana sa ran ƙarin bayani zai biyo baya kan wannan lamari.

Afrika, Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Najeriya Ta Jinjinawa Saudiya
Next Post: NAHCON Ta Fitar Da Jadawalin Hajjin Bana 2027

Karin Labarai Masu Alaka

An Yi Barazanar Kaurace Wa Gasar Cin Kofin Duniya Labarai
Jirgin Ruwan ‘Yan Gudun Hijira Ya Nitse Kogi A Tunisiya Labarai
Rasha Da Ukraine Sun Cigaba Da Yakar Juna Afrika
Sojojin Kasar Uganda Sun Bazama Neman Bobi Wine Sakamakon Rikicin Bayan Zabe Siyasa
Cutar Zazzabin Lassa Tayi Ajalin Mutum 1 Yayinda Mutane 11 Suka Kamu A Jihar Gombe Najeriya
Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Babban Sakataren MDD Yayi Allah Wadai Da Matakin Soja A Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Shirin Dare 26.11.2025 Rediyo
  • Majalisar Dattawar Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet Labarai
  • Dan Takarar Gwamna Na Jam’iyyar APM A Bauchi Ya Bada Gudummawar Naira Miliyan ₦21 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Bara Da Shira Labarai
  • An Kashe Mutane 169 A Wani Harin Sudan Ta Kudu Afrika
  • Trump Da Bin Salman Da Wasu Kasashe Za Su Sa Hannu A Rikicin Sudan Labarai
  • CAN: Da Alamu Daliban St. Mery Na Cikin Koshin Lafiya Najeriya
  • Gwamnatin Najeriya Ta Dauki Matakai Don Farfaɗo Da Maɗaba’ar Gwamnati Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.