Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

NAHCON Ta Fitar Da Jadawalin Hajjin Bana 2027
Published: April 28, 2026 at 7:29 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: April 29, 2026

Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON), ta ce a ranar 3 ga watan Mayun shekarar 2026 ne za a fara jigilar maniyyata daga Najeriya zuwa Kasar Saudiyya, domin gudanar da ibadar aikin Hajjin bana.

NAHCON ta sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Yaɗa Labarai, Fatima Sanda Usara, ta fitar, inda ta ce jirgin farko na kamfanin FlyNas zai tashi daga sabon filin jirgin sama na Kasa-da-Kasa na Gateway da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Baya ga jihar Ogun, sauran jiragen da za su tashi a wannan rana sun haɗa da Kamfanonin Umza da Max Air, da za su kwashe maniyyatan jihohin Kogi da Nasarawa daga Abuja, sai Kamfanin Air Peace da zai kwashe maniyyatan jihar Oyo daga Legas.

Kazalika daga Birnin Kebbi, wani jirgin na FlyNas zai tashi da maniyyatan Jihar Kebbi.

Tuni jami’an NAHCON da suka haɗar da tawagar likitoci suka sauka a ƙasar Saudi Arabiya a ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, domin yin shirye-shiryen tarɓar maniyyatan Najeriya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Tinubu Ya Sayi Fom Din Takarar Shugaban Kasa
Next Post: Matasa Sun Sayawa Ferfesa Pantami Fom Din Takarar Gwamnan Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

ECOWAS Ta Saka Dokar Ta Baci A Afrika Ta Yamma Afrika
Wata Mace Ta Mutu A Hannun ‘Yan-Fashin Daji, Wata Ta Haihu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Turkiyya Ta Zargi Alakar Isra’ila Da Somaliya Afrika
Ministan Tsaron Najeriya Badaru Yayi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugaban Kasar Uganda Yana Kokarin Mayar Da Mulkin Kasar Na Gado Labarai
Afirka Ta Kudu Da Kenya Sun Bayyana Yaudarar ‘Yan Kasashe Da Yawa Tare Da Sakasu Yaki Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Anyi Taho Mugama Tsakanin ‘Yan Sandan Turkiyya Da ‘Yan Kungiyar ISIS Afrika
  • Anfara Tantance Lafiyar Maniyyatan Jihar Gombe Kiwon Lafiya
  • Rikici Ya Barke A Kano Bayan Kashe Wani Matashi Da Ake Zargi Da Kashe Ladani Najeriya
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najib Razak Zai Kara Shekaru 15 A Gidan Yari Saboda Cin Zarafin Kujerar Mulki Labarai
  • Ankara Gano Wani Abu Mai Kama Da Abun Fashewa A Jabo Jihar Sokoto Tsaro
  • JEI Da Abokan Hulɗar Sun Gudanar Da Aikin Shuka Itatuwa Domin Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya Afrika
  • An Fara Dawo Da Alhazain Najeriya Gida Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.