Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Amurka Ta Yi Juyin Mulki A Kasar Venezuela
Published: January 3, 2026 at 10:52 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 3, 2026

Amurka ta hambare gwanatin shugaba Maduro a Venezuela, kuma tace zata gudanar da harkokin kasar har zuwa lokacin da ya dace. Shugaban Amurka Donald Trump ne ya bayyana haka a wani taron da manema labarai a Mar-Largo, wurin shakatawarsa dake jihar Florida.

Da manema labarai suka matsa neman karin bayani kan yadda Amurka zata tafiyar da harkokin kasar ta Venezuela, shugaba Trump bai bada amsa kai tsaye ba. Yace “zamu tafiyarda harkokin kasar da gungun mutane. Kuma zamu tabbatar da cewa an tafiyar da kasar yadda ya kamata.” inji shugaban na Amurka.

Da ‘yan jarida suka matsa don jin yadda za’a aiwatar da shirin, shugaba Trump, yace “ana yin haka a halin yanzu.” Muna zabar mutane. Muna magana da mutane. Kuma za mu sanar da ku ko su wanene wadan nan mutanne, inji shugaba Trump.

Da yake magana a taron na manema labarai, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, yace, Maduro ba shine halataccen shugaban Venezuela ba. Domin tun a shekara ta 2020 zamanin gwamnatin Trump ta farko Amurka ta tuhumi Maduro, haka itama gwamnatin Biden da kuma gwamnatiin Trump ta yanzu.

A taro da manema labaran, shugaba Trump ya gargadi shugaban kasar Columbia cewa ya shiga taitayinsa. Yana zarginsa da sarrafawa da safarar miyagun kwayoyi,  Da aka tambayeshi gameda kasar Cuba, shugaba Trump, yace akwai bukatar ita ma Cuba a dubi lamarinta domin tana bukatar taimako.

Da suke maida martani kan wannan mataki, wakkilan majalisar dokokin Amurka ‘yan jam’iyyar Democrat, sunce jami’an gwamnati Trump basu gaya musu gaskiya ba a ganawarda suka yi da su a baya bayan nan gameda Venezuela, suko jami’an bangaren zartaswa sun fada musu basu da burin sauya gwamnati a Venezuela.

 

Amurka, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Farashin Dalar Amurka Ya Tashi Ranan Juma’a
Next Post: Kasashen Duniya Sunyi Tir Da Hambarar Da Gwamnatin Venezuela

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaban Amurka Yayi Watsi Da Tattaunawar Kawo Karshen Yaki Da Iran Afrika
Za’ayi Jana’izar Marigayi Ali Khamenei a Tehran, Qom da Mashhad Afrika
Shahararren Dan Dambe Anthony Joshua Yayi Hatsarin Mota A Jihar Ogun Labarai
Shugaba Tinubu Ya Yabawa Dakarun Tsaro Bisa Ceto Matar Marigayi Janar Rabe Afrika
Iran Tace Farisa Zata Kai Hari Kan Mayakan Amurka Amurka
Gurbin Yaya Tongo: INEC Ta Tsayar Da 19 Ga Satumba Don Zaɓen Cike Gurbi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Amurka Tabada Tabbacin Bawa Ukraine Tsaron Shekarun 15 Amurka
  • Tinubu Ya Rantsar Da Shugabar Hukumar FCC Najeriya
  • Gwamnatin Tarayya Tana Neman Kudi Domin Aiwatar Da Kasafin Kudin 2026 Najeriya
  • Libya Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasashen Faransa Da Amurka Afrika
  • Mayakan M23 Sun Tsagaita Wuta A Gabashin Kwango Labarai
  • Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Zata Karbi ‘Yan Gudun Hijirar Da Amurka Ta kora Afrika
  • Najeriya Da Amurka Sun Amince Su Haɗa Kai Don Inganta ’Yancin Addini Da ƙarfafa Tsaro A Nijeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Alhassan Yayi Nasarar Kifar Da Wurkilili A Gasar Damben Gargajiya Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.