Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Zamfara: Sai Mun Hada Kai Don Kawo Karshen Ta’addanci
Published: February 18, 2026 at 3:56 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin jihar Zamfara a Najeriya ta ƙaddamar da sabbin motocin yaƙi masu sulke (Armoured Personnel Carriers APCs) tare da gabatar da ingantaccen tsarin jiragen sama marasa matuƙi na sa-ido (Unmanned Aerial Systems – UAS), a wani muhimmin mataki na ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Gwamnan jihar, Dauda Lawal, ne ya jagoranci sayo motocin da sauran kayan aikin tsaro, a cewar gwamnatin, domin aiwatar da manufofinsa na magance matsalolin tsaro, musamman barazanar ‘yan bindiga da hare-haren makamai da suka shafi al’ummomi da dama a cikin jihar a ‘yan shekarun nan.

Bikin ƙaddamar da kayan aikin ya gudana ne a Fadar Gwamnatin jihar dake Gusau, inda Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya jagoranci kaddamarwar tare da jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatocin jihohi da hukumomin tsaro na tarayya wajen tinkarar matsalolin tsaro.


Sabbin kayan aikin da aka ƙaddamar sun haɗa da motocin yaƙi masu sulke da kuma jiragen sama marasa matuƙi na zamani, waɗanda Gwamnatin Jihar Zamfara ta tanada domin tallafa wa ayyukan rundunar ‘yan sanda da sojoji, musamman a fannonin sa-ido, gano maɓoyar masu laifi, da kuma saurin kai ɗauki a lokutan gaggawa.

Manyan baƙi da suka halarci taron sun haɗa da ‘yan Majalisar Dokokin jihar Zamfara, kwamishinoni, masu ba gwamna shawara na musamman, shugabannin gargajiya da na addini, jagororin siyasa, da shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnati sannan kuma, manyan hafsoshin tsaro da shugabannin hukumomin tarayya masu aiki a jihar sun kasance cikin mahalarta taron.


Jami’an gwamnati sun bayyana cewa haɗa motocin yaƙi masu sulke da fasahar jiragen sa ido na zamani zai ƙara inganta tattara bayanan sirri, saurin kai farmaki kan masu aikata laifi, da kuma dawo da kwarin gwiwar al’umma kan tsarin tsaron jihar.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Najeriya Da Haɗin Guiwar Gwamnatin Jihar Zamfara Suna Shirin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Jihar
Next Post: Gwamnatin Kano Ta Rufe Gidajen Bukukuwa Da Shakatawa

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Za A Rantsar Da Mainasara Kogo A Matsayin Shugaban Kundin Da’ar Ma’aikata Labarai
‘Yan Tawayen Kasar Kwango Ne Suka Kai Hari Filin Jirgin Saman Kisangani Labarai
Masu Ruwa Da Tsaki 60 Sun Samu Horon Sasanta Rikici Don Ƙarfafa Zaman Lafiya Afrika
Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki Labarai
Mutane 13 Sun Mutu Inda Wasu 57 Suka Jikkata A Barundi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Kebbi Ta Samu Tankokin Yaki Tsaro
  • Kamfanin Magani Na Aspen Yayi Gagarumar Asara A Cinikayya Afrika
  • Kocin Ranchers Bees Ya Yi Murabus Wasanni
  • Fiye Da Mutane 10 Sun Mutu A Hatsarin Hanyar Kano Labarai
  • Amurka Tana Cigaba Da Kare Jami’in Da Ya Kashe Ba Amurke Amurka
  • Sanarwar MDD Ya Nuna Aniyar Mayakan RSF Na Kisan Kare Dangi Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika
  • ‘Yan Kasar Venuzuela Zasu Fara Komawa Gida Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.