Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Kasar Saudiya Zatayi Gwajin Noman Dabino A Kano
Published: February 15, 2026 at 1:43 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ma’aikatar Muhalli ta Tarayyar Najeriya ta zaɓi jihar Kano domin aiwatar da shirin gwajin Bunƙasa Dabino da King Salman Humanitarian Aid and Relief Centre (KSrelief) ta gabatar.

Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar Kano, Dakta Dahir M. Hashim, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano bayan karɓar baƙuncin wakilan KSrelief.

Hashim ya ce an zaɓi Kano ne saboda yanayin ta mai dacewa da noman dabino da kuma muhimmancin dabino a al’ada da addini a cikin al’umma.

Ya bayyana cewa shirin zai yi amfani da sabbin dabarun shuka tare da haɗa ƙwararru daga Saudiyya da kuma masana daga Jihar Kano domin tabbatar da zurfin ilimi da musayar ƙwarewa.

Dakta Hashim ya lura cewa shirin ba wai na shuka itatuwa kaɗai ba ne, illa dai wani cikakken aikin raya ƙasa ne da ke da amfani ta fuskar muhalli, tattalin arziki da zamantakewa.

Ya kuma buƙaci tawagar da ta zo da ta tabbatar da haɗa al’umma sosai domin ƙarfafa mallaka da dorewar shirin a nan gaba.

A ƙarshe, ya sake jaddada cewa ma’aikatar a shirye take ga duk wata haɗin gwiwa mai inganci da za ta ƙarfafa juriya da samar da hanyoyin samun abin yi ga al’umma.

Labarai, Najeriya, Sana'o'i

Post navigation

Previous Post: Channels TV: Ta Yi Rashin Hazikin Dan Jarida Mr Khani
Next Post: Amurka Ta Kai ‘Yan Cirani Kamaru

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Donald Trump Ya Nada Shugaban Bankin Tarayya Amurka
Gwamnatin Najeriya Tace Ta Farmaki Mayakan ISIS A Jihar Sokoto Labarai
APC Ta Yi Babban Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya Najeriya
‘Yan Bindiga Sun Kashe Dan Gaddafi A Gidansa Dake Kasar Libya Afrika
Tattalin Arzikin Kasar Uganda Zai Bunkasa A Wannan Shekarar Labarai
‘Yan Bindiga Sun Karya Alkawarin Dakatar Da Kai Hare Hare A Najeriya Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Dawo Da Kudaden Ma’aikata Afrika
  • Hawan Durba A Fadar Sarkin Zazzau Afrika
  • ‘Yan Sandan Najeriya Sunyi Nasarar Hallaka ‘Yan Ta’adda A Katsina Afrika
  • Kasar Tanzaniya Zata Gina Babban Tashar Iskar Gas Labarai
  • Hanyar Gombe Dukku Darazo Ta Zamo Abun Damuwa Ga Al’ummar Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • Magungunan Cutar Kolera Sun Makale A Dubai Afrika
  • An Gudanar Da Tiyatar Ido Kyauta A Gombe Afrika
  • Wasu Lauyoyi Sunyi Murabus Yayin Gudanar Da Wata Shari’a A Kasar Amurka Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.