Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Ranar Lahadi Anyi Zaben Shugaban Kasa A Congo
Published: March 16, 2026 at 7:52 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

A Jamhuriyar Congo an kada kuri’a a zaben shugaban kasa ranar Lahadi, wanda ake sa ran zai tsawaita wa’adin mulkin shugaba Denis Sassou Nguesso, daya daga cikin shugabannin Afirka da suka fi dadewa akan karagar mulki, duk kuwa da cewar mutane basu fito da yawaba don kada kuri’unsu.

Sassou na fuskantar wani kalubale daga abokan hamayya, tare da saka wasu fitattun jagororin adawa na kasar a gidan yari, wasu kuma suna gudun hijira. Jam’iyyun adawa da dama sun kauracewa zaben, suna masu cewa tsarin ba shi da inganci.

Fiye da ‘yan Kwango miliyan 3.2 ne aka yi wa rajista don kada kuri’a, ko da yake masu sharhi da kungiyoyin fararen hula sun yi hasashen cewa za a kada kuri’u kusan kashi 68 cikin dari da aka samu a shekarar 2021, lokacin da Sassou ya lashe wa’adinsa na shekaru biyar da suka gabata da kashi 88.4% na kuri’un.

Wani ya shaidawa Reuters cewa, an samu gajerun layuyuka na masu kada kuri’u a mafi akasarin rumfunan zabe a Brazzaville babban birnin kasar.

Bayan da ya kada kuri’arsa a Brazzaville, Sassou ya shaidawa manema labarai cewa yana fatan kwarin gwiwar da ya ce ya gani a fagen yakin neman zabe za ta fito fili a sakamakon karshe.

“Muna fatan abin da na ji a duk lokacin yakin neman zabe zai tabbata a yau,” in ji shi.

Afrika, Labarai, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Za’a Jima Ana Fama Da Tsadar Farashin Mai
Next Post: Jagoran Adawar Uganda Bobi Wine Ya Fice Daga Kasar

Karin Labarai Masu Alaka

Matasa Sun Sayawa Ferfesa Pantami Fom Din Takarar Gwamnan Gombe Afrika
Libya Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasashen Faransa Da Amurka Afrika
Bayan Ya Ziyarci Kwankwaso Gawuna Zai Karbi Katin ADC Afrika
‘Yan Bindiga A Mali Sun Kashe Direbobin Manyan Motoci Afrika
Amurka Zatayi Amfani Da Sansanonin Birtaniya Amurka
Rikici Tsakanin NNPC Da Kungiyar Gwamnoni Akan Gibin Kudade Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Ukraine Zata Sayi Iskar Gas Daga Mozambique Afrika
  • Jam’iyyar APC Ta Ayana Jamilu Gwamna A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Gombe Afrika
  • Hukumar NAPTIP Ta Kubutar Da Yara 11 Daga Hannun Masu Safara Mutane Labarai
  • Ana Cigaba Da Samun Hare Hare Da Jiragen Marasa Matuki A Sudan Labarai
  • Shugaba Tinubu Ya Taya Musulmai Murnar Sallah, Tare Da Kira Zuwa Ga Kishin Kasa Afrika
  • An Kashe Mutane 169 A Wani Harin Sudan Ta Kudu Afrika
  • Amurka Da Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Sun Fara Wata Tattaunawa Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.