Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Kungiyoyin Mata A Jihar Filato Sunyi Gangamin Samun Jagorancin Siyasa
Published: March 31, 2026 at 6:32 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kungiyoyin mata a jihar Filato sun bi sahin takwarorinsu a fadin Najeriya wajen yin gangami don kara karfafa bukatar su na neman kujeru saba’in da hudu a majalisar wakilan Najeriya.

Kujeru na musamman wa mata a majalisar wakilan Najeriya, wanda aka fi sani da HB1349, mataimakin kakakin majalisar wakilan Najeriya, Honarabul Benjamin Okezie da wassu ‘yan majalisar su goma sha biyu ne suka gabatar sa kudirin.

Kudirin yana neman sauya kundin tsarin mulki na alibi dari tara da tasa’in da tara ne don samar da karin kujeru wa mata, don magance karancin wakilcin mata a majalisun dokoki, da yanzu yake kasa da kashi biyar.

Honarabul Esther Dusu, tsohuwar ‘yar majalisa ce a majalisar dokokin jihar Filato wacce kuma ta jagoranci gangamin, tace abinda suke bukata shine samun gurabe da zasu taimaka wa mata.

Madam Selina Ali, shugaban kungiyar majalisar kungiyoyin mata a Najeriya, NCWS, reshen jihar Filato tace rashin mata a majalisu ya sanya ba’a jin muryoyinsu da bukatunsu.

Shugaban kungiyar mata musulmi ta FOMWAN, reshen jihar Filato, Hauwa Umar Musa tace guraben da aka ba mata, har yanzu basu wadatar ba.

Itama Madam Sarah Dalut, Shugaban kungiyar matan Kirista a jihar Filato, tace ba fada suke yi da maza ba, suna dai bukatar samun karin kaso ne.

Shugaban kungiyar ‘yan jarida mata a Jihar Filato, Grace Akwe Gotip ta karfafa aniyar bada gudunmowar ganin mata sun furta matsalolin su don samun gyara.

A defender guda kuwa, mamba mai wakiltar Jos ta Arewan Arewa a majalisar dokokin jihar Filato, Adamu Aliyu yace suna kan kokarin samarda dokokin da zasu ba mata ‘yanci.

Bayanai na nuni da cewa mata a Najeriya na da kujeeru ishirin da daya ne kachal daga cikin kujeru dari hudu da sittin da tara a majalisun dokokin kasar, a kididdiga ta karshen shekara ta dubu biyu da ishirin da biyar.

Daga Jos Wakiliyar GTA Hausa Amurka Ke Magana Zainab Babaji tana dauke da cikekken rahoton

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/03/AUD-20260331-WA0012.mp3

 

Afrika, Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: An Saka Dokar Hana Fita A Jos Ta Arewa
Next Post: Bayan Ya Ziyarci Kwankwaso Gawuna Zai Karbi Katin ADC

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumar IMF Tana Naziri Domin Kara Bada Lamuni Ga Kasar Zambiya Afrika
Gwamnonin Arewa Sunyi Allah Wadai Da Harin Jos Afrika
Birtaniya Ta Bukaci Israela Ta Janye Shawarar Fadada Iko Da Kogin Jordan Labarai
Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yayi Murabus Afrika
Wata Biyu Najeriya Bata Bada Lasisin Shigo Da Mai Daga Ketare Ba Labarai
An Gudanar Da Tiyatar Ido Kyauta A Gombe Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Faransa Zata Bunkasa Nukiliyarta Afrika
  • Jihar Ekiti Ta Aiwatar Da Dokar Haraji Najeriya
  • Wata Tankar Mai Ta Kife A Apapa Legas Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • INEC: Akwai Yiwuwar Dage Zaben 2027 Saboda Azumi Labarai
  • Jakadan Kasar Sin a Najeriya Ya Ziyarci Tinubu Najeriya
  • Rashin Tsaro: Gwamnati Ta Bada Umarnin Daukar Ma’aikata Sama Da 94,000 Najeriya
  • Mutane Da Yawa Ke Mutuwa A Dalilin Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba Kiwon Lafiya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.