Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

An Bude Gasar Kwallon Kafa Ta Mata A Najeriya NWFL 2025
Published: November 27, 2025 at 9:23 PM | By: Bala Hassan

An bude Gasar Firimiya ta Mata NWFL 2025

A ranar Laraba 26 ga watan Nuwamban 2025, a bude Kakar gasar Firimiya ta Mata ta Najeriya (NWFL) da wasanni a Cibiyoyi tara a fadin Najeriya.

Wasan da aka yaye labule a hukumance a filin wasa na Samson Siasia da ke Yenagoa, inda zakarun gasar Bayelsa Queens suka yi nasara a kan masu rike da kambun gasar 2024 Edo Queens da ci 3-2.

A Makurdi, Adamawa Queens ta fara kakar wasa da kafar dama, inda ta doke Pacesetter Queens da ci 2-0 ta kafar Ifeoma Damian da Mary Sunday.

Yayin da Ƙungiyar Heartland Queens ta yi nasara a Owerri, inda ta doke Ekiti Queens da ci 2-1, sakamakon bugun daga kai sai mai tsaron gida.

A Abuja, ƙungiyar Ibom Angels ta yi kunnen doki da Naija Ratel.

Ƙungiyar Nasarawa Amazons, wadda ta zo ta biyu a kakar wasa ta bara, ta samu nasa da ci 2-1 akan Delta Queens.

A Iyamho, Abia Angels ta tashi canjaras 2-2 da Confluence Queens.

A Akure, FC Robo Queens ta samu nasara mai mahimmanci a kan Sunshine Queens da ci 1-0, a bugun daga kai sai mai tsaron gida daga Marvellous Oladuni.

A wasan da akayi a Onikan da ke Legas, Dannaz Ladies ta doke Osun Babes da ci 3-2.

A Umuahia, sabbin haurowa gasar Ahudiyannem Queens sun yi canjaras 0-0 da Remo Stars Ladies, wanda hakan ya kawo ƙarshen wasan farko mai cike da tarihi a tsakiyar mako.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: ECOWAS Da AU Sun Nuna Damuwa Kan Juyin Mulki A Guinea-Bissau
Next Post: Muna Kira Ga Kasashen Duniya Su Sa Baki Don A Saki Mohamed Bazoum

Karin Labarai Masu Alaka

Onana Ba Ya Cikin Tawagar Kamaru (AFCON) Wasanni
Najeriya Ta Mika Koke Ga FIFA Tana Zargin DR Congo Ta Sanya ‘Yan Wasan Da Basu Cancantaba Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Sabon Jadawalin Gasar Kwalon Kafa Ta Turai 2026 Wasanni
CAF Ta Yanke Hukunci Kan Ƙasashen Senegal Da Moroko AFCON 2025 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Real Madrid: Ta Kori Xabi Alonso Bayan Rashin Nasara A Wasan Kofin Sfaniya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Alhassan Yayi Nasarar Kifar Da Wurkilili A Gasar Damben Gargajiya Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ukraine Takai Hari Wajen Kera Makami Mai Linzami A Rasha Labarai
  • Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi Afrika
  • Sojojin Najeriya Sun Kwato Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Najeriya
  • Gwamna Abba Ya Gana Da Kwankwaso Kamun Ganawarsa Da Tinubu Siyasa
  • APC Ta Yi Babban Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya Najeriya
  • Gwamnatin Tarayya Na Kokarin Hana Demokraɗiyya A Najeriya Siyasa
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC Siyasa
  • Mamakon Ruwan Sama Da Iska Ya Hallaka Mutane Uku A Jihar Yobe Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.