Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi Afrika
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya Afrika
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91 Afrika
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu Afrika
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika

Gwamnatin Kano Ta Rufe Gidajen Bukukuwa Da Shakatawa
Published: February 18, 2026 at 4:46 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta bada da umarnin rufe dukkan wuraren bukukuwa wato event centre da na shaƙatawa a fadin jihar.

Hakazalika hukumar ta hana kidan DJ da kuma gidajen gala yayin da aka fara azumin watan Ramadan.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

“Daga ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026, duk irin waɗannan wurare (cibiyoyin nishaɗi) za su kasance a rufe har zuwa ƙarshen watan Ramadan mai alfarma.

“Umarnin zai fara aiki daga ƙarfe 10:00 na dare a ranar (Laraba),” in ji sanarwar.

A cewar hukumar, an ɗauki matakin ne domin bai wa al’umma damar gudanar da azumin Ramadan da ayyukan ibadarsu cikin kwanciyar hankali ba tare da wata katsalandan ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa rufewar za ta ci gaba a duk tsawon lokacin azumi, yayin da za a sanar da ranar sake buɗe wuraren, musamman a lokacin bukukuwan Sallah, a lokacin da ya dace.

Hukumar ta buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki su ba da cikakken haɗin kai tare da bin umarnin bisa dokar da ta kafa ta.

Ta kuma jaddada cewa matakin na daga cikin aikinta na tabbatar da bin ƙa’idojin da suka shafi harkokin nishaɗi a jihar.

Hukumar ta yi addu’ar Allah Ya ba da zaman lafiya da lafiya a lokacin gudanar da ibadar watan mai alfarma, tare da roƙon Allah Ya sa kowa ya shaida watan cikin rahama da arziki.

Labarai, Najeriya, Nishadi

Post navigation

Previous Post: Zamfara: Sai Mun Hada Kai Don Kawo Karshen Ta’addanci
Next Post: Shugaba Bola Tinubu Ya Saka Hannu A Dokar Zabe

Karin Labarai Masu Alaka

Kungiyar EU Zata Taimakawa Somalia Da Kudade Labarai
Tawagar Shirya Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe Ta Ziyarci Masarautun Jihar Labarai
An Yi Barazanar Kaurace Wa Gasar Cin Kofin Duniya Labarai
Menene Illar Yada Labaran Karya A Kafofin Sada Zumunta Na Zamani Labarai
Farashin Danyen Mai Da Iskar Gas Ya Tashi Afrika
Meyasa Israela Take Hana Kaiwa Gaza Kayan Tallafi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Birtaniya Zata Fara Raba Rigakafin Allurar Cutar Sankara Kimiya
  • Shugaba Trump Ya Bukaci A Cigaba Da Zanga Zanga A Iran Labarai
  • Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS Afrika
  • Mun Kwato Kimanin Naira Biliyan 40 Na Badakala A Tsawon Shekara Daya Labarai
  • Isra’ila Takai Hare Hare Birnin Tehran Afrika
  • An Katse Intanet Da Wayar Tarho A Kasar Uganda Siyasa
  • Ukraine Da Syria Zasuyi Haɗin Gwiwar Tsaro Labarai
  • Ferfesa Pantami Yasamu Tikitin Takarar Gwamnan Gombe A Jami’yar PDP Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.