Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC
Published: February 9, 2026 at 10:22 PM | By: Bala Hassan

Abdu Mai Kaba Ya Ajiye Aikin Horas da Wikki Tourist fc Bauchi da ke Arewa maso gabas a Najeriya.

Bayan da ƙungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist fc Bauchi ta tashe canjaras da Katsina United 4-4 a wasan mako na 25 cikin gasar Firimiyar lig na Najeriya 25/26.

Ƙungiyar ta shiga rudani bisa irin maki da ta ke zubarwa a gida Wikki Tourist tayi canjaras a wasannin gida har guda 7 an shata a wasa daya a kakar wasan bana, jimillan makin da tayi a sara a gida 17, wadda hakan ya zamo babban kalu-bale a ƙungiyar kuma tana mataki na 15 da maki 29.

Inda wasu ki zargin maihoras da yanwasa Abdu Maikaba na rashin sanya Yan wasa a lokacin da ya dace, har ya kaima wasu magoya bayan Kulub din sukan fadi bakaken maganganu akan sa a zahiri da kuma shafin sada zumunta (Social media ) .na cin mutumcin sa

Saidai wasu masharhanta na gani cewa babu laifin Maikaba matsalar Wikki matsalace ta cikin gida, domin duk Shugaban da aka sauke yana da magoya baya da zasu tsangwami sabon shugaba suma a bangaren sabon babu shiri da wadda ya samesu a ciki musamman ƙungiyar Magoya baya saboda nan ta ke shima sabon shugaba zai sauke Jagororin magoya baya shima ya nada nasa wannan na daya daga cikin matsalolin Wikki ” inji masharhanta a jihar.

“Kuma anki ayi zaben Shuwagabannin magoya baya kamar yadda doka ya tanardar sai dai a bada rokon kwarya.

A gefe guda kuwa masu ruwa da tsaki akan harakar kwallon kafa a jihar wadda dasu aka kirkiri ƙungiyar sun daura laifine akan yadda aka sauka daga tsari da dokokin da aka kafa ƙungiyar.

Abdu Maikaba shi ya dawo da ƙungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist zuwa buga gasar Firimiyar lig na Najeriya

Abdu Maikaba Ya Ajiya Aikinsa a Wikki Tourist
Ga abunda ya rubuta

 

 

 

 

 

 

 

“Ina so in yi amfani da wannan dama domin sanar da hukumar gudanawar kungiyar Wikki Tourists F.C game da shawarar da na yanke na yin murabus daga matsayina na babban mai horaswa (Technical Adviser) na kungiyar, tun daga 09/02/2026 “inji Maikaba

Wannan shawara ta zama dole ne sakamakon dalilai kamar haka:

Rashin hadin kai:
Akwai rashin jituwa tsakanin masu ruwa da tsaki na kungiyar, wanda hakan ke sanya wahalar cimma manyan burin na kungiyar da ta sanya a gaba.

Saboda tsaron lafiya na ina fuskanci
barazanar a yayin gudanar da aikina daga wasu bangarorin magoya bayan kungiyar, bisa yadda suke mun a fili da kuma ta kafafen sada zumunta inji shi.

Saboda wadannan dalilai, na ga ya dace in dauki matakin ajiye aiki bayan na nemi shawarar iyalina.

Ina kuma amfani da wannan dama domin gode wa hukumar gudanawar kungiyar bisa damar da suka bani nayin aiki a wannan babban kulob. Ina fatan za a karbi murabus dina.

 

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Kasashen Daular Larabawa Tare Da Saudiya Da Jordan Sunyi Allah Wadai Da kasar Israel
Next Post: Yawan Mai Da Kasashen OPEC Suke Hakawo Yayi Kasa Sosai

Karin Labarai Masu Alaka

Sauya Sunan Lafarge Africa Zuwa HBM Nigeria Plc Zai Samar Da Cigaba – Sarkin Fulanin Gombe Afrika
Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Ya Zamo Khalifan Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Pantami Ya Bayyana Dalilin Mayar Da Zaben Sa Abuja Afrika
Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Bayan Ya Ziyarci Kwankwaso Gawuna Zai Karbi Katin ADC Afrika
  • Hukumar NAHCON Ta Bude Asibiti A Madina Afrika
  • Jirgin Ruwan ‘Yan Gudun Hijira Ya Nitse Kogi A Tunisiya Labarai
  • Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Jita-Jitar Yunkurin Sanya Wa Tinubu Guba A Abinci Afrika
  • Tinubu Ya Buƙaci Gwamnoni Su Mutunta Hukuncin Kotun Ƙoli Kan ’Yancin Kuɗin ƙananan Hukumomi Labarai
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Emmanuel Macron: Yakamata Wani Sashi Ya Rika Takawa Wani Sashi Birki A Tsarin Demokradiya Amurka Amurka
  • Iran Ta Tsagaita Kai Hare Hare Makwabta Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.