Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ANNOUR Ta Raba Kayan Makaranta Na CFA Miliyan 5.5 Ga Yara A Douala Afrika
  • Sabbin Shugabannin NUJ Bauchi Sun Sha Alwashin Inganta Aikin Jarida Afrika
  • INEC Ta Ce Zaɓen Gombe, Kwami Da Funakaye Yana Gudana Cikin Lumana Afrika
  • GOSERC Ta NemI Haɗin Kan Masu Ruwa Da Tsaki Wajen Inganta Wutar Lantarki A Gombe Afrika
  • Ranar Zaman Lafiya: Pastor Yohanna Buru Ya Jagoranci Tawagar Kiristoci Zuwa JNI Kaduna Afrika

Zaɓen Gombe: ’Yan Sanda Sun Sanar Da Tsauraran Matakan Tsaro Ranar Asabar
Published: September 18, 2026 at 1:52 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe ta ce ta tura isassun jami’ai da kayan aikin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron zaɓen cike gurbin kujerar Majalisar Wakilan Tarayya ta Gombe-Kwami-Funakaye da za a gudanar ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2026.

Rundunar ta ce an shirya matakan tsaron ne tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro da ke ƙarƙashin Kwamitin Tuntuɓar Hukumomin Tsaro Kan Zaɓe, ICCES.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya bayar da umarnin tura jami’ai da kayan aikin tsaro zuwa ofisoshin INEC, cibiyoyin tattara ƙuri’u, rumfunan zaɓe da sauran muhimman wurare a ƙananan hukumomin Gombe, Kwami da Funakaye.

Rundunar ta ce za a takaita zirga-zirga tare da rufe harkokin kasuwanci a ƙananan hukumomin uku daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma ranar zaɓe, sai dai ayyukan da suka shafi muhimman hidimomin jama’a.

Ta kuma bayyana cewa ma’aikatan da ke gudanar da muhimman ayyuka ba za su yi amfani da ƙahon mota na musamman ba, motoci marasa rajista ko motocin da aka rufe lambobin rajistarsu.

Rundunar ta ƙara da cewa jami’an hukumomin tsaro da aka amince da su ƙarƙashin ICCES ne kawai za su samar da tsaro a lokacin zaɓen. Ta ce ba za a ba ƙungiyoyin tsaro na jiha, ƙungiyoyin tsaro masu zaman kansu, jami’an tsaro na kamfanoni ko ƙungiyoyin sa-kai damar gudanar da aikin tsaro a zaɓen ba.

’Yan sanda sun kuma yi gargaɗi kan yaɗa labaran ƙarya, daba, tashin hankali, ɗaukar makamai ko wasu abubuwan da ka iya haddasa rashin zaman lafiya a rumfunan zaɓe.

Rundunar ta buƙaci iyaye da masu kula da matasa da su gargaɗi ’ya’yansu da kada su bari a yi amfani da su wajen tayar da hankali ko aikata laifuka a lokacin zaɓen.

Ta ce duk wanda aka kama yana aikata wani abu da ka iya kawo cikas ga gudanar da zaɓen cikin lumana, za a kama shi kuma a gurfanar da shi gaban kotu.

Rundunar ta buƙaci al’ummar Gombe da su ba jami’an tsaro haɗin kai tare da kai rahoton duk wani abin da suke zargi zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa ko kuma ta lambobin gaggawa 0815 056 7771 da 0903 643 5359.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ne ya sanya hannu kan sanarwar a madadin Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Gombe.

Afrika, Labarai, Najeriya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Zaɓen Gombe-Kwami-Funakaye: INEC Ta Buƙaci Masu Zaɓe Da Jami’ai Su Bi Dokoki
Next Post: INEC Ta Ce Zaɓen Gombe, Kwami Da Funakaye Yana Gudana Cikin Lumana

Karin Labarai Masu Alaka

Jirgin Ruwan ‘Yan Gudun Hijira Ya Nitse Kogi A Tunisiya Labarai
Shugaba Tinubu Yasa Hannu Kan Dokar Kasafin 2026 Afrika
Kasar Gambiya Ta Gayawa Kotun MDD Shirin Myanmar Akan Musulmai Afrika
Sojoji Sunkai Farmaki Gidan Dan Adawa A Kasar Uganda Bobi Wine Afrika
Farashin Man Fetur Yakara Tashi Labarai
Anyi Rashin ‘Yan Jarida 6 A Jihar Gombe Sakamakon Hatsarin Mota Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ANNOUR Ta Raba Kayan Makaranta Na CFA Miliyan 5.5 Ga Yara A Douala
  • Ƙungiyoyin Fararen Hula Sun Ƙarfafa Yaƙi Da Gurɓacewar Muhalli A Kaduna
  • Sabbin Shugabannin NUJ Bauchi Sun Sha Alwashin Inganta Aikin Jarida
  • INEC Ta Ce Zaɓen Gombe, Kwami Da Funakaye Yana Gudana Cikin Lumana
  • Zaɓen Gombe: ’Yan Sanda Sun Sanar Da Tsauraran Matakan Tsaro Ranar Asabar

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • FIFA Ta Yi Wa Malaysia Kaca-kaca Wasanni
  • Kotu A Najeriya Ta Kame Mutane Bisa Zargin Ta’addaci Afrika
  • GTA Hausa Logo
    Shirin Dare 2030 UTC Yau Juma’a 11.21.2025 Rediyo
  • Farashin Mai A Kasuwannin Duniya Yayi ƙasa Kadan Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Fubara Yana Yiwa Dimokraɗiyya Zagon Kasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sojoji Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda a Kukareta Afrika
  • Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Shirya Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Jihar Filato Afrika
  • Magoya Bayan Manchester United Sun Bukaci A Siyar da Bruno Fernandes Bayan Rashin Nasara A Kan AC Milan Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.