Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Shirya Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Jihar Filato
Published: May 9, 2026 at 3:45 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Operation Enduring Peace ta shirya taro na musamman da masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomin Jos ta Gabas, Bassa da Jos ta Arewa a jihar Filato, domin tabbatar da zaman lafiya don gudanar da ayyukan noma a daminar bana cikin lafiya da kwanciyar hankali.

Kamandan runduna ta uku kuma kwamandan Operation ENDURING PEACE, Manjo Janar Folusho Oyinlola, ya yi kira da mahalarta taron su sake sabunta alkawarin samar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar kananan hukumomin Jos ta Arewa, Jos ta Gabas, da Bassa.

Da yake jawabi ta bakin babban hafsan hafsoshin rundunar Birgediya Janar Senlong Sule, game da muhimmancin taron na masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Jos, GOC ya jaddada cewa taron ya zama wajibi don samar da hanyoyin zaman lafiya a yayin da ake fara noma.


A wata sanarwa da kakakin rundunar zaman lafiya ta Operation Enduring Peace, Keftin Chinonso Polycarp Oteh, Kwamandan ya yabawa mazauna kananan hukumomin 3 bisa jajircewar da suka yi na tabbatar da zaman lafiya, tare da bayyana raguwar tashe-tashen hankula a ‘yan watannin da suka gabata, yana mai alakanta zaman lafiyar da aka samu wajen ci gaba da tattaunawa da hadin kan al’umma.

Kwamandan ya kuma ja hankalin masu ruwa da tsakin kan a cigaba da taimatawa wajen tabbatar da ci gaba da aka samdadon kare yankunan daga barazanar tsaro da ke kunno kai.

Manjo Janar Oyinlola ya bayyana damuwarsa dangane da sace-sacen mutane, hare-haren da ake kai wa masu hakar ma’adanai, da kera makamai ba bisa ka’ida ba, da kuma yawaitar kwararowar shanu zuwa yankunan manoma, wanda a tarihi ya kai ga lalata gonaki da kuma daukar fansa da rarrabuwar kawuna dake wanzuwa tsakanin al’umma.

Kazalika, Kwamandan ya bayyana cewa a kwanakin baya babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya amince da turo bataliya ta musamman zuwa jihar Filato da nufin hanzarta shawo kan barazanar da ke kunno kai da kuma karfafa kokarin tabbatar da zaman lafiya da ake ci gaba da yi, wanda tuni ya fara rage fargaba da kai hare-hare a yankin.

Da yake jawabi ga sarakuna da shugabannin addinai da na al’umma da suka halarci taron, GOC ya jaddada muhimmancin karfafa hanyoyin magance rikice-rikicen da suka shafi al’umma, inda ya bukaci masu ruwa da tsaki da su wayar da kan matasan su kan abubuwan da za su tunzura su, kamar barnar gonaki ko sanya guba wa shanu tare da karfafa samar da ka’idojin da al’umma za su bi.

Ya kuma yi kira ga kafafen yada labarai da su yi amfani da ka’idojin da aikinsu ya shimfida, yana mai gargadin cewa rahotanni masu ban sha’awa ko wadanda ba a tabbatar da su ba, sau da dama suna haifar da tashin hankali maimakon gina zaman lafiya.

A karshen jawabinsa, Manjo Janar Oyinlola ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro na gudanar da aikinsu na zama masu sasantawa don tabbatar da tsarin mulkin kasa da kuma kare duk wani dan kasa mai bin doka da oda ba tare da la’akari da kabila ko addini ba.

Ya kuma tunatar da taron cewa zaman lafiya wata bukata ce ta gama-gari ba tare da nuna goyon baya ga wasu ba, inda ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa Operation ENDURING PEACE za ta ci gaba da gudanar da ayyukan kawar da maboyar masu aikata laifuka, wanda yace hakan ya dogara ne kacokam kan tabbatar gaskiya da hadin kan al’ummomin yankin.

A nasa bangaren shugaban karamar hukumar Jos ta Arewa Barr. John Kyohroh Christopher ya yaba wa OPERATION ENDURING PEACE da suke aiki ba dare ba rana wajen ganin an samu zaman lafiya a karamar hukumar, bayan kashe-kashen da ya auku a Anguwan Rukuba.

Christopher ya bayyana cewa karamar hukumar za ta ci gaba da hada kai da rundunar, domin tabbatar da zaman lafiya a Jos ta Arewa.

Ya kuma yabawa GOC da shugaban hafsan soji da kuma babban hafsan hafsoshin tsaro bisa rabon tallafin taki ga manoman yankin.

Sarakunan yankin da shugabannin al’ummar Musulmi da Kirista, sun yaba da kokarin da sojoji suke yi, inda suka yi alkawarin tabbatar da cewa za’a gudanar da ayyukan noma cikin kwanciyar hankali.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Dakaru Sun Hallaka ’Yan Ta’adda Masu Yawa – DHQ
Next Post: Jam’iyar SDP Tana Gudanar Da Babban Taro A Bauchi

Karin Labarai Masu Alaka

Za A Rantsar Da Mainasara Kogo A Matsayin Shugaban Kundin Da’ar Ma’aikata Labarai
Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Borno Tsaro
Sanata Goje Yayi Watsi Da Fidda ‘Yan Takarar APC A Gombe Afrika
Ministan Yaɗa Labarai: Ceto Daliban Neja An Samu Natsuwa A Kasa Labarai
Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Aika Sammaci Dr. Yusuf Baba-Ahmed Labarai
Fadar Sarkin Musulmi: Talata Ne 1 Ga Watan Sha’aban Na 1447AH Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Tinubu Ta Karyata Kafa Kamfanin Gwal A Legas Labarai
  • AFCON 2025, Jerin Abubuwan Da Aka Haramta Wa Magoya Baya Wasanni
  • Birtaniya Ta Bukaci Israela Ta Janye Shawarar Fadada Iko Da Kogin Jordan Labarai
  • Kasar Ukraine Tayi Watsi Da Shiga Kungiyar NATO Labarai
  • Ga Dukkan Alamu Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Bai Kare Ba Sauran Duniya
  • Kasar Zimbabwe Ta Samar Da Dokar Tsawaita Mulkin Mnangagwa Zuwa 2030 Labarai
  • Idan Allah Yasa Muka Kafa Gwamnati Zamu Kyautata Wa Ma’aikata Yakubu Adamu Dan Takarar Kujeran Gwamnan Bauchi Labarai
  • Wani Bayahude Ya Harbe Bafalatsine Dan Shekaru 16 Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.