Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ANNOUR Ta Raba Kayan Makaranta Na CFA Miliyan 5.5 Ga Yara A Douala Afrika
  • Sabbin Shugabannin NUJ Bauchi Sun Sha Alwashin Inganta Aikin Jarida Afrika
  • INEC Ta Ce Zaɓen Gombe, Kwami Da Funakaye Yana Gudana Cikin Lumana Afrika
  • Ranar Zaman Lafiya: Pastor Yohanna Buru Ya Jagoranci Tawagar Kiristoci Zuwa JNI Kaduna Afrika
  • Burkina Faso Ta Fara Kera Motocin Yaƙi Afrika

GOSERC Ta NemI Haɗin Kan Masu Ruwa Da Tsaki Wajen Inganta Wutar Lantarki A Gombe
Published: September 17, 2026 at 6:22 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Jihar Gombe, Gombe State Electricity Regulatory Commission (GOSERC), ta gudanar da taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin wayar da kansu kan hurumin hukumar, manufofinta da kuma nauyin da aka dora mata.

Taron da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Gombe, ya samu halartar wakilan kungiyoyi daban-daban, ciki har da Ƙungiyar Masu Nika Gyada, Ƙungiyar Masu Samar da Ruwan Sha a Roba, COREN, ASUU, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki.

Da yake buɗe taron, Kwamishinan Ma’aikatar Makamashi da Albarkatun Ƙasa na jihar Gombe, Alhaji Sanusi Ahmad Maidalan Pindiga, ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin mataki a ƙoƙarin jihar na samun ’yancin kai a fannin makamashi, bunƙasa masana’antu da haɓaka tattalin arziƙi.

Kwamishinan ya ce kafa GOSERC ya samu ne bisa tanadin doka da kundin tsarin mulki da kuma Dokar Wutar Lantarki ta 2023, wadda ta bai wa jihohi damar taka muhimmiyar rawa wajen tsara da kuma kula da kasuwannin wutar lantarki a jihohinsu.

Ya ce Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ɗauki matakin kafa GOSERC domin rarraba ikon kula da harkokin wutar lantarki, tare da bai wa Jihar Gombe damar kula da tsarin kasuwar wutar lantarki a cikinta.

Tun da farko, Shugaban GOSERC, Alhaji Abba Arabi, ya ce an shirya taron ne domin cimma manufofin da aka kafa hukumar a kansu.

Ya bayyana cewa taron ya kasance wata dama ta sanar da masu ruwa da tsaki game da hurumin hukumar, tare da ba su damar bayar da shawarwari kan yadda za a samar da ingantaccen tsarin kula da wutar lantarki a jihar.

Kwamishiniyar Kula da Harkokin Shari’a ta hukumar, Barrister Talatu Abubakar, ta tabbatar wa mahalarta taron cewa za a duba tare da tantance dukkan shawarwari da ra’ayoyin da ƙungiyoyin da suka halarci taron suka gabatar, domin la’akari da yiwuwar aiwatar da su.

Shi ma wakilin Babban Hakimin Gombe, Alhaji Sammani Babba, ya bayyana kafa GOSERC a matsayin wani muhimmin ci gaba a tarihin bunƙasa Jihar Gombe.

Wakilan Ƙungiyar Masu Nika Gyada, Ƙungiyar Masu Samar da Ruwan Sha a Roba, ASUU da COREN sun bayyana goyon bayansu ga hukumar tare da alkawarin ba ta haɗin kai wajen cimma manufofinta.

Mataimakin Shugaban hukumar, Injiniya Suleman Usman, da Kwamishinan Harkokin Fasaha, Abubakar Sa’ad, sun kuma yi wa mahalarta bayani kan ayyukan hukumar, ciki har da dangantakarta da kamfanonin rarraba wutar lantarki da kuma masu amfani da wutar.

A yayin taron, mahalarta sun gabatar da tambayoyi da shawarwari musamman kan samar da wutar lantarki, tsarin kula da ita, matsalolin masu amfani da wutar da kuma ayyukan Kamfanin Savannah Electricity Company.

Hukumar ta amsa tambayoyin da aka gabatar tare da tabbatar da aniyarta ta samar da ingantaccen, sahihi kuma mai gaskiya tsarin kula da wutar lantarki wanda zai kuma kare muradun masu amfani da wutar lantarki a jihar Gombe.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Ranar Zaman Lafiya: Pastor Yohanna Buru Ya Jagoranci Tawagar Kiristoci Zuwa JNI Kaduna
Next Post: Zaɓen Gombe-Kwami-Funakaye: INEC Ta Buƙaci Masu Zaɓe Da Jami’ai Su Bi Dokoki

Karin Labarai Masu Alaka

An Kashe Mutum 2 Da Suka Ba ‘Yan-Matan (GGCSS Maga) Kariya! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Za’a Fassara Hudubar Arfa Da Harshen Hausa Afrika
Mace Ta Farko Da Zata Shugabanci Jami’ar Northwest Dake Kano Najeriya
Barau Jibril: Mu Ba ‘Yan Amshin Shata Bane A Majalisa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Mali Da Burkina Faso Za Su Haramta Wa Amurkawa Izinin Shiga Ƙasashen Su Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Tinubu Ya Rantsar Da Shugabar Hukumar FCC Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ANNOUR Ta Raba Kayan Makaranta Na CFA Miliyan 5.5 Ga Yara A Douala
  • Ƙungiyoyin Fararen Hula Sun Ƙarfafa Yaƙi Da Gurɓacewar Muhalli A Kaduna
  • Sabbin Shugabannin NUJ Bauchi Sun Sha Alwashin Inganta Aikin Jarida
  • INEC Ta Ce Zaɓen Gombe, Kwami Da Funakaye Yana Gudana Cikin Lumana
  • Zaɓen Gombe: ’Yan Sanda Sun Sanar Da Tsauraran Matakan Tsaro Ranar Asabar

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Najeriya Ta Samar Da Wuta Mai Aiki Da Hasken Rana A Jami’ar ADUSTECH Afrika
  • Yakin Iran Da Isra’ila Da Amurka Zai Shafi Kasashen Afirka – Masana Afrika
  • Hukumar NDLEA Ta Kama Wata Mata Da cikin Bogi Na ƙwaya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • China Da Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Sun Kulla Yarjejeniya Afrika
  • Matar El-Rufai Ta Roƙi Tinubu Ya Tabbatar An Yi Wa Mijinta Adalci Afrika
  • Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Aika Sammaci Dr. Yusuf Baba-Ahmed Labarai
  • Shugaba Putin Ya Bukaci Kawo Karshen Yaki Da Iran Afrika
  • Zelensky Na Ukraine Zai Gana Da Takwaransa Na Faransa A Yau Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.