Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

An Kashe Mutum 2 Da Suka Ba ‘Yan-Matan (GGCSS Maga) Kariya!
Published: November 17, 2025 at 5:41 PM | By: Yusuf Aliyu Harande | Updated: November 17, 2025

A wani harin da ‘yan-bindiga suka kai a cikin daren jiya Assabar, wayewar garin yau Lahadi a wata sakandaren ‘Yan Mata dake garin Maga wato (GGCSS Maga) a karamar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi Yan Bindigar sunyi garkuwa da Dalibai Mata 25 tare da kisan Mataimakin Shugaban Makarantar.
Al’umar garin Maga da  na Makarantar yanzu haka suna cikin firgici da damuwa sakamakon faruwar Lamarin.
Mazauna yankin sun ce maharan sun farwa makarantar ne da daddare, inda suka gudanar da aika-aikar su ba tare da wata ta gargada ba, kamar yada wata mazauniyar unguwar Murjanatu Hassan Gishiri ta bayyana lamarin a matsayin wani abin takaici da ya jefa daukacin masarautar Zuru cikin alhini.
Wani magidanci da ya zanta da gidan rediyon Amurka ke Magana yace an harbe mataimakin shugaban makarantar Malam Hassan Yakubu Makuku lokacin da yake kokarin kare daliban, yayinda wani ma’aikacin Makarantar Malam Ali Shehu, ya samu raunin harbin bindiga a hannu shi.
Rumdunar ‘Yan sandan jihar Kebbi a ta bakin mai magana da yawun ta CSP Nafi’u Abubakar ya tabbatar da faruwar Lamarin tare da bayyana cewa an sace dalibai 25 a yayin samamen.
A cewar rundunar ‘yan sandan, an tura tawagar hadin gwiwa ta rundunonin ‘yan sanda, da sojoji, da ‘yan banga domin binciken hanyoyin ‘yan bindigar a dazuzzukan da ke kusa da su da nufin ceto daliban tare da kamo maharan.
Kwamishinan ‘yan sanda Bello M. Sani ya tabbatar wa mazauna yankin kudurin hukumar na kare rayuka da dukiyoyi. Ya kuma bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, su kuma lura, tare da tallafa wa ayyukan tsaro a yayin da ake ci gaba da bincike da ceto daliban.
Wasu mazauna yankin sun tabbatar da hakan a wata zanta da  suka yi da GTA Hausa, sun ce Jiragen Sojin Saman Najeriya na cigaba da shawagi a yankin, lamarin da ke nuna Dakarun Sojin sun fara aikin ceto Daliban.
Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Lauya Bala: Tabbas Kotu Zata Soke Zaben Shugaban PDP, Turaki
Next Post: An Yanke Hukuncin Kisa Ga Hasina Tsohuwar Firaiy-Ministan Bangladash

Karin Labarai Masu Alaka

Jam’iyar SDP Tana Gudanar Da Babban Taro A Bauchi Afrika
Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna Afrika
Makokin Ashura: An Gudanar Da Taron Tunawa Da Aliyul Asghar A Gombe Afrika
’Yar Kasuwa Ta Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Hari Da Saurayinta Ya Kai Mata Afrika
Kotun Tarayya Ta Yankewa Nnamdi Kanu Daurin Rai-da-Rai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Tinubu Zai Gabatar Da Jawabi ga Shugabannin Duniya A Taron UNGA Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ambaliyar Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutum 13 A Malawi Labarai
  • Ukraine Ta Tura Tawagar Kwarerru Zuwa Kasashen Larabawan Domin Basu Kariya Labarai
  • Isra’ila Zata Karbi Mutanenta A Yankin Gaza Labarai
  • Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Christ Musa Ministan Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Umar Aliyu, Shugaban Magoya Bayan Wikki Tourist
    Jagorancin Wikki Tourist FC Na Samun Yabo Wasanni
  • Rasha Ta Yiwa Amurka Tayin Daina Bada Bayanan Sirri Afrika
  • Hukumar NAPTIP Ta Kubutar Da Yara 11 Daga Hannun Masu Safara Mutane Labarai
  • Najeriya Da Kasar Saudiya Sun Kulla Yarjejeniyar Tsaro Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.