Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

CBN: An Samu Ƙaruwar Masu Cin Bashin Banki Basa Biya
Published: January 20, 2026 at 4:42 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Bankuna a Najeriya sun bayar da rahoton karuwar rashin biyan bashi a daga magidanta da kamfanoni duk da cewa samuwar rance da bukatar sa sun karu, a cewar binciken yanayin bashi na babban bankin Najeriya (CBN) na zangon karshe na 2025.

Rahoton ya nuna cewa rashin biyan bashi ya karu a dukkan nau’ikan rance, ciki har da rancen dake da jingina da wanda bai da jingina, da kuma na kamfanoni.

Kananan gidaje da kamfanoni kanana sun fi fuskantar matsala saboda hauhawar farashi, tsadar makamashi, da karancin kudin shiga.

A bangaren manyan kamfanoni, rashin biyan bashi ya kai kashi 6% a wasu lokuta, yayin da sauran kamfanonin kudi suka samu matsakaicin rashin biyan bashi na kashi 6.2%, lamarin da ke nuna tsanani a bangarorin tsarin kudi.

Duk da haka, bankuna sun kara bayar da rance ga gidaje da kamfanoni, amma babban bankin Najeriya ya yi gargaɗin cewa karuwar rashin biyan bashi na iya lalata ingancin kadarori da rage karfin bankuna.

CBN ta kuma ba da shawarar inganta tsarin dawo da bashi da kiyaye ka’idojin banki don rage matsalar.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Tinubu Ta Karyata Kafa Kamfanin Gwal A Legas
Next Post: Hukumar NAHCON Ta Kamallah Shirye Shiryen Hajjin 2026 A Kasar Saudiya

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Kano: Zamu Kara Daukar Malamai Domin Inganta Ilimi Najeriya
Hukumar EFCC Ta Kama Dan Kasuwa A Kamaru Afrika
Majalisar Wakilai Tayi Allah Wadai Da Hare-Haren ‘Yan Bindiga A Gombe Labarai
‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Cin Karensu Babu Babbaka A Najeriya Afrika
Lauya Bala: Tabbas Kotu Zata Soke Zaben Shugaban PDP, Turaki Najeriya
GOSEMA Ta Horar Da Mambobin LEMCs A Jihar Gombe Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamna Fubara: Rashin Kariya daga PDP Ne Ya Tilasta Ni Komawa APC Siyasa
  • Ukraine Ta Tura Tawagar Kwarerru Zuwa Kasashen Larabawan Domin Basu Kariya Labarai
  • Shugaban Kasar Uganda Yana Kokarin Mayar Da Mulkin Kasar Na Gado Labarai
  • Harin Bom Din Maiduguri Ya Kashe Mutane Biyar Ya Raunata Fiye Da Talatin Najeriya
  • Hukumar DSS Ta Sake Kama Abubakar Malami Labarai
  • Matar El-Rufai Ta Roƙi Tinubu Ya Tabbatar An Yi Wa Mijinta Adalci Afrika
  • Afirka Ta Kudu Zata Fuskanci Koma Baya A Bangaren Samar Da Ayyukanyi Afrika
  • Jiragen Ruwa Suna Biyayya Ga Dokar Hana Ketare Ruwa Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.