Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Published: March 1, 2026 at 4:32 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

An sanar da nadin Mojtaba Khamenei a matsayin sabon Jagoran Juyin Juya Halin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, jin kadan bayan rasuwar tsohon jagoran ƙasar, Ali Khamenei.

Sabon jagoran ya gaji muƙamin ne a wani lokaci mai cike da ƙalubale a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ake fuskantar takaddama mai tsanani tsakanin Iran da wasu ƙasashe, ciki har da Israel.

A cikin sakonsa na farko ga al’umma, Mojtaba Khamenei ya bayyana cewa manufofin ƙasar Iran na ci gaba da shirinta na makamashin Nukiliya da kuma tsayawa tsayin daka wajen kare muradunta a yankin ba za su sauya ba. Ya jaddada cewa Iran za ta ci gaba da bin tafarkin da aka gada daga jagorancin da ya gabata.

Ya kuma yi nuni da cewa ƙasar na cikin shiri da cikakken tsaro, yana mai bayyana Iran a matsayin ƙasa mai ƙarfin guiwa wadda take da isassun dabaru da ƙarfin kare kanta daga duk wata barazana ta waje.

Masu sa ido kan harkokin siyasar duniya na kallon wannan sauyi a matsayin wani sabon babi a tarihin jagorancin Iran, musamman a daidai lokacin da ake fama da rikice-rikice da takaddama a yankin Gabas ta Tsakiya.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa
Next Post: Amurka Da Isra’ila Sunkai Hari Kan Iran

Karin Labarai Masu Alaka

Dalibin Jami’a Ya Rasa Ransa A Birnin Dakar Yayin Zanga Zanga Afrika
Tarayyar Turai Zasu Kirkiro Sojojin Haɗin Gwiwa Labarai
Ahmed Gara Ya Kaddamar da Kofin Sarkin Gombe, Ya Jaddada Bunƙasa Matasa Afrika
Gwamnatin Kebbi Ta Samu Tankokin Yaki Tsaro
Masar Ta Jibge Jiragen Yaki Marasa Matuka Afrika
Jama’ar Kasar Iran Sun Bayyana Goyon Baya Ga Ayatollah Mojtaba Khameni Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Bahrain Ta Gabatar Da Kudurin Sulhu Ga MDD Afrika
  • Anyi Jana’izar Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo Afrika
  • Kimanin Mutane 200 Ne Suka A Mutu A Wani Harin Jirgin Yakin Sojin Najeriya Afrika
  • Farashin Mai A Kasuwannin Duniya Yayi ƙasa Kadan Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Manoma Suna Fuskantar Barazanar Karyewa A Kasar Ghana Afrika
  • Majalisar Wakilai Ta Rikon Kwaryar Nijar Ta Gudanar Da Zama Karo Na Biyu Afrika
  • Shugaban Lebanon Ya Nemi Gudanar Da Shawarwari Kai Tsaye Afrika
  • Sanata Sa’idu Alkali Ya Kaurace Wa Zaben Fidda Gwani Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.