Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Bayan Shekaru Biyar, Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Gano Motar da Aka Sace A Fatakwal
Published: June 20, 2026 at 9:49 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar, ya bayyana cewa jami’an Sashen Binciken Sirri (SID) na rundunar, tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), sun gano motar ne yayin wani aikin tantance bayanan motoci a Ofishin Ba da Lasisin Motoci na Hukumar Haraji ta Jihar Gombe a ranar 8 ga Yunin 2026.

Sanarwar ta ce yayin binciken bayanan motar mai lambar rajista FH823PHC, an gano alamun da suka nuna cewa motar na da alaƙa da rahoton sata.

Binciken farko ya tabbatar da cewa motar mallakin Misis Cecilia A. Duru ce, mazauniyar Akwaka Lane da ke Rumuodumaya a Fatakwal, kuma an sace ta ne a ranar 17 ga Satumban 2021.

Binciken da rundunar ta gudanar ya nuna cewa an kai motar zuwa Jamhuriyar Nijar a shekarar 2023. Daga bisani kuma an dawo da ita Najeriya ta Karamar Hukumar Illela da ke Jihar Sokoto a ranar 17 ga Oktoban 2025.

Bayan haka, an sayar da motar a Jihar Kaduna kafin daga ƙarshe a kawo ta Gombe domin sake yi mata rajista.

Rundunar ta ce bincike na ci gaba da nufin gano tare da cafke duk waɗanda ake zargi da hannu a satar motar da kuma safararta ba bisa ƙa’ida ba.

Haka kuma, rundunar ta tabbatar wa al’umma da cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyi, tare da jan hankalin masu sayen motoci da su tabbatar da sahihancin takardun mallaka da bayanan mota daga hukumomin da suka dace kafin su kammala ciniki.

Sanarwar ta ƙara da cewa za a sanar da jama’a duk wani sabon ci gaba da aka samu yayin da bincike ke gudana.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Makokin Ashura: An Gudanar Da Taron Tunawa Da Aliyul Asghar A Gombe
Next Post: Gwamnatin Tarayyar Najeriya Zata Raba Taki Ga Manoma

Karin Labarai Masu Alaka

Rundunar Tsaro Suna Cigaba Da Nasara Akan ‘Yan Ta’adda Tsaro
Najeriya Ta Bawa Dan Takarar Guinea-Bissau Mafaka Afrika
Gidauniyar Sultan Ta Jaddada Muhimmancin Kula Da Lafiyar Yara A Gombe Afrika
Kasar Saudiya Zata Cika Azumi Talatin Kimiya
An Yankewa Prime Ministan Kasar Tunisiya Hukuncin Shekaru 24 A Gidan Yari Afrika
Kungiyar Tsaro Ta NATO Tana Fuskantar Kalubale Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sanata Goje: Sakamakon Zaben Daga Abuja Zai Fito Afrika
  • Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Gana Da Shugaba Tinubu Siyasa
  • Babu Alamar Tsagaita Wuta A Yakin Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Manchester United: Za Ta Nada Michael Carrick A Matsayin Kocin Riƙon ƙwarya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji A Kauyen Wanka Jihar Filato Afrika
  • Kasashen Da Suke Kawance Da Amurka Sun Juyawa Trump Baya Afrika
  • Isra’ila Tace Bazata Sake Kai Hari Kan Cibiyar Gas Ta Iran Ba Afrika
  • Sarkin Musulmi Ya Ziyarci Shugaba Bola Tinubu Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.