Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Iran Tabada Tabbacin Cigaba Da Rufe Mashigar Hormuz
Published: March 13, 2026 at 8:01 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Iran ta bada tabbacin ci gaba da yaki tare da rufe mashigin Hormuz a matsayin abin da za ta iya kaiwa ga Amurka da Isra’ila, in ji sabon Jagoran juyin juya halin Musulunci Mojtaba Khamenei a ranar Alhamis a cikin kalaman farko da aka danganta shi da shi tun bayan da ya gaji mahaifinsa da aka kashe.

Khamenei bai bayyana da kansa ba kuma wani mai gabatarwa na gidan talabijin na kasar ne ya karanta jawabin. Ba a fitar da wani hotonsa ba tun bayan harin da Isra’ila ta kai a farkon yakin da ya yi sanadiyar mutuwar yawancin iyalansa, ciki har da mahaifinsa da matarsa.

Sanarwar ta jiya Alhamis ta dau hankali, inda Khamenei ya yi kira ga kasashen da ke makwabtaka da Iran da su rufe sansanonin Amurka da ke yankinsu tare da gargadin cewa Iran za ta ci gaba da kai musu hari.

“Ina tabbatar wa kowa da kowa cewa ba za mu yi sakaci da daukar fansar jinin shahidan ku ba,” in ji malamin nan mai tsaurin ra’ayi wanda ke da kusanci da babbar rundunar sojan Iran.

Khamenei ya kara da cewa, “Bukatar da jama’a ke da, ita ce mu ci gaba da samar da ingantaccen tsaro da kuma sanya makiya su yi nadama. Dole ne a ci gaba da yin amfani da shingen toshe mashigin ruwa na Hormuz,” Khamenei ya kara da cewa, yayin da yake magana kan hanyar jigilar kayayyaki da kashi biyar na man duniya ke bi ta gabar tekun Iran.

Afrika, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Amurka Da Kasashen Yamma Suna Cigaba Da Kai Ruwa Rana Akan Nukiliyar Iran
Next Post: Gwamnatin Amurka Na Kokarin Watsi Da Tsohuwar Dokar Jones

Karin Labarai Masu Alaka

Kamfanin Bitcoin A Korea Ta Kudu Yayi Kuskuren Turawa Masu Mu’amala Da Kamfanin Kudade Afrika
Guguwa Mai Karfi Ta Raunata Dubban Mutane A Madagascar Labarai
Tsananta Hukunci Ga Masu Fyade Kan Takaita Cin Zarafin Yara Labarai
NAHCON Ta Kaddamar da Tawagar Malamai Afrika
An Kaddamar Da Jigilar Maniyyata Aikin Hajji A Abuja Afrika
Amurka Zata Kara Tura Sojoji Gabas Ta Tsakiya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Za’a Ninka Shekarun Zama A Gidan Kurkuku Ga Masu Auren Jinsi A Senegal Afrika
  • Tsohon Ma’aikacin VOA Saleh Shehu Ashaka Ya Rasu Afrika
  • Yakin Gabas Ta Tsakiya Ya Haifar Da Tsadar Taki Da Mai Ga Manoma Labarai
  • ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji 15 Da Wasu Fararen Hula A Benin Afrika
  • Netanyahu Ya Umarci Rundunar Sojoji Takara Fadada Ayyukanta A Lebanon Afrika
  • Wakilan Majalisar Dokokin Phillipines Suna Yunkurin Tsige Shugaban Kasar Afrika
  • An Kashe Mutane 25 Yayin Kai Wasu Hare Hare Jihar Adamawa Labarai
  • Pakistan Zata Karbi Bakwancin Saudiya, Turkiyya Da Masar Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.